Kada a Sake Bari Masu Satar Kuɗin Talakawa Su 'Ci Banza', Buhari Ya Gargaɗi Ɓangaren Shari'a
- Shugaba Muhammadu Buhari ya ce duk wata shari’ar rashawa da aka samu matsala wurin uzurorin ayyukanta, alamar tambaya ce ga jajircewar ma’aikatan shari’ar wurin yaki da rashawa
- A cewarsa, wajibi ne a kama duk wanda aka samu da laifin rashawa da duk wasu laifuka na zagon kasa ga tattalin arziki, kuma a yi gaggawar gurfanar da mai laifin da gamsassun hujjoji don ya fuskanci hukunci
- Ya yi wannan furucin ne jiya a Abuja yayin bude wani taro na kwana uku da aka yi don wayar da kan ma’aikatan shari’a, masu bincike akan rashawa da masu zartar da hukunci
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce duk wata shari’ar rashawar da aka samu matsala a wurin ayyukanta saboda wasu uzurori, alama ce ta tambaya dangane da jajircewar ma’aikatan shari’ar kasar nan wurin yaki da rashawa.
Ya ce kada a dagawa duk wanda aka kama da rashawa, zagon kasa ga tattalin arzikin kasa da kuma duk wani laifi na kudi kafa daga fuskantar fushin hukuma.
Jiya ya sanar da hakan a wurin wani bude wani taro na kwana uku da za a yi a Abuja musamman don wayar da kan ma’aikatan shari’a, masu bincike akan rashawa da kuma mahukunta, mai lakabin ‘Aiwatar da Shari’a: Babbar hanyar yaki da Laifukan zangon kasa ga tattalin arziki.’
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mustapha ya ce shari’a ta jajirce, kada ta zama ‘yar kallo
Buhari wanda ya samu wakilci Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha ya ce ma’aikatan shari’a su yi kokarin cikashe duk wasu gurabun sharia da masu laifukan cikin jama’a su ke boyewa a cikinsu.
Ya kara da jan kunne, inda ya ce:
“Kada shari’a ta tsaya a matsayin ‘yar kallo yayin da masu laifi su ke amfani da damar wurin tserewa da dukiyoyinmu, su kara karfi sannan su bai wa wasu kwarin-gwiwar shiga harkar rashawa.”
Shugaban Hukumar Yaki da Rashawa da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Zagon Kasa, EFCC, Abdulrasheed Bawa, ya ce EFCC ta shiga damuwa akan yadda ake fadi shari’ar rashawa saboda wasu uzurori na ayyukan shari’a, kamar yadda Daily Trust ta nuna.
Bawa ya ce hakan na iya kawo kokwanto a zuciyoyin mutane
A cewarsa:
“A matsayinmu na hukuma, ba ma sa ran mu ne za mu ci duk wata shari’ar da mu ke yi da wani, amma akwai lokutan da EFCC da ‘yan Najeriya da dama su ke tafka asara akan wasu matakai na shari’a inda wanda ake zargin ya sace kudin al’umma ke samun damar komawa gida ya mori kudaden da ya samu akan wasu azurorin shari’a.
“Akwai yiwuwar hakan ya sanya kokwanto a zuciyoyin jama’a musamman yadda su ka amince da gaskiyar shari’ar Najeriya a ciki da wajen kasar.”
Asali: Legit.ng