'Yan IPOB Sun Kashe Wata Mata Mai Juna Biyu, Yaranta 4 Da Wasu 'Yan Arewa 6 a Anambra
- Mayakan IPOB a ranar Lahadi sun halaka wata mata, yaranta 4 da kuma wasu mutane 6, duk ‘yan arewa a Jihar Anambra
- Sun halaka matar wacce ta ke dauke da juna-biyu a Isulo, cikin karamar hukumar Orumba ta arewa da ke jihar ba tare da ta yi musu komai ba
- Sarkin Hausawan yankin, Alhaji Sa’id Muhammad a jiya ya koka inda ya ce ‘yan arewa da ke zama a jihar sun yanke shawarar tserewa
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Jihar Anambra - A ranar Lahadi, Mayakan IPOB sun halaka wata mata mai juna biyu, yaranta 4 da kuma wasu mutane 6, wadanda duk ‘yan arewa ne da ke zama a Jihar Anambra, Daily Trust ta ruwaito.
Sun halaka matar, wacce ke dauke da juna-biyu da yaranta ne a Isulo, karamar hukumar Orumba ta Arewa a jihar.
Kashe-kashen wani sabon salon ta’addanci ne da ‘yan IPOB su ke kan yi wa wadanda ba asalin ‘yan jihar ba, kuma har sojoji da ‘yan sanda ba su bari ba.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Hatta asalin ‘yan Jihar Anambra da kuma ‘yan yankin Kudu maso Gabas ba su kyale ba tun da can saboda burinsu na kafa kasar Biafra.
Sai dai bayan sa’o’i 48 da kashe-kashen ranar Lahadi wanda aka dinga halaka ‘yan arewa ba tare da sun yi komai ba, babu wata jarida ko gidan talabijin da su ka wallafa labarin duk da yadda hotunan su ka bazu a kafafen sada zumunta da kuma caccakar da jami’an tsaro, kungiyoyi da mutane su ka dinga yi.
Kashe-kashen ‘yan arewan da kungiyar, mai keta dokoki ta yi ya auku ne bayan kwanaki kadan da bayyanar dan majalisar Jihar Anambra wanda ‘yan ta’adda su ka sace.
Farmakin ranar Lahadi
Sarkin Hausawan karamar hukumar Orunba ta arewa, a jiya ya koka akan harin, inda ya ce ‘yan arewa mazauna Jihar Anambra sun yanke shawarar barinta saboda yadda mambobin Kungiyar Tsaron Gabas (ESN) ta mayakan IPOB a kullum su ke halaka musu ‘yan uwa.
A tattaunawar da Daily Trust ta yi da Muhammad, ya ce halaka matar mai juna biyu da yaranta hudu ba sabon abu ba ne a wurinsu saboda an dade ana halaka musu mutane ta irin wannan salon.
Ya ci gaba da cewa:
“Matar asali ‘yar Jihar Adamawa ce. Kafin rasuwarta, ta zauna a Orumba ta Kudu ne kuma a ranar Lahadi ta je kai wa wasu kawayenta ziyara ne tare da yaranta hudu.
“A hanyarta ta komawa gida aka halaka ta. An daukota a babur din haya, daga nan ‘yan bindigan su ka kai musu farmaki, su ka halaka ta da yaranta hudu yayin da mai babur din ya tsere.”
An ga bidiyon gawawwakin matar da yaranta da aka halaka
A wani bidiyo wanda Daily Trust ta gani a Twitter, wadanda aka halaka su na kwance a kasa cikin jini, jikinsu duk harsashi, sai aka ji wani ya na magana da harshen Ibo ya na cewa:
“Kowa ya kalli wannan bidiyon, sun harbi wata mata da yaranta hudu. Duk ‘yan arewa ne, harbin duk wanda su ka gani a hanya su ke yi; don haka kowa ya kula.”
Wakilin Daily Trust ya ruwaito cewa a ranar Alhamis din sun halaka ‘yan acaba biyar sannan sun babbake baburansu a karamar hukumar Onocha. An kai gawawwakin hudu daga cikinsu ma’adanar gawa yayin da su ka babbaka gawar daya.
Daily Trust ta ruwaito cewa a cikin kwanakin karshen mako an babbake wata babbar mota wacce ta shiga Kudu da kaya yayin da aka halaka direban da wasu. Yanzu haka direbobin manyan motoci da ke kudu maso gabas sun ce a tsorace su ke harkoki a yankin.
'Batanci: Ba Za Mu Lamunci Kashe Kiristoci a Bauchi Ba Da Sunan Zagin Annabi, CAN Ta Ja Kunnen Musulmi
Akwai wadanda ke boye masu laifi
A ranar Litinin, Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Echeng E. Echeng ta zargi mazauna jihar da rufa wa masu laifin asiri. Ya bayyana hakan ne yayin tattaunawa da manema labarai akan kisan dan majalisar Jihar Anambra, Okechukwu Okoye da hadiminsa, Cyril Chiegboka.
Daily Trust ta ruwaito cewa mayakan IPOB sun lashi takobin ci gaba da halaka ‘yan majalisar Jihar Anambra.
Ya ce ana kiran masu laifi da ‘yan bindigan da ba a san su ba, alhalin akwai wadanda su ka san su. Kuma akwai jami’an tsaron da ke rufa asirin masu laifin wanda hakan ba daidai ba ne.
'Yan Sanda Sun Cafke Matashin Da Ke Kai Wa 'Yan Bindigan Neja Abinci
A wani rahoton, Rundunar ‘yan sandan Jihar Neja ta kama wani matashi mai shekaru 20, Umar Dauda wanda ake zargin yana kai wa ‘yan ta’adda kayan abinci a jihar, The Punch ta ruwaito.
A wata takarda wacce jami’in hulda da jama’an rundunar ‘yan sandan jihar, Wasiu Abiodun ya sanya wa hannu, an samu bayani akan yadda aka kama matashin bayan mazauna yankin sun bayar da bayanan sirri ga hukuma.
Kamar yadda takardar tazo:
“An yi kamen ne a ranar 16 ga watan Maris din 2022, da misalin karfe 11 na dare bayan samun bayanan sirri akan yadda ake yawan ganin wani mai kai wa ‘yan ta’adda kayan abinci a kauyen Kapako da ke Lapai.”
Asali: Legit.ng