Yanzun Nan: Gwamnonin Jam'iyyar PDP Uku Sun Saka Labule da Obasanjo

Yanzun Nan: Gwamnonin Jam'iyyar PDP Uku Sun Saka Labule da Obasanjo

  • Tsohon shugaban ƙasa Obasanjo ya shiga ganawar sirri da wasu gwamnonin jam'iyyar PDP guda uku a gidansa da ke Abeokuta
  • Gwamna Wike na Ribas da gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo da gwamna Ortom ɓa Benuwai ne suka kai wa Obasanjo ziyara
  • Tsohon shugaban ƙaaa ya ƙara jaddada cewa a yanzu shi ba ɗan siyasa bane, ya zaɓi zama wani masoyin yan siyasa

Ogun - Gwamnoni uku na jam'iyyar hamayya PDP sun shiga ganawar sirri da tsohon shugaban ƙasa a Najeriya, Olusegun Obasanjo, a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun.

Daily Trust ta ruwaito cewa gwamnonin uku da suka sa labule da Obasanjo sune; Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas, Seyi Makinde na jihar Oyo da gwamna Samuel Ortom na jihar Benuwai.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Aisha Buhari, Ministar mata da matar mataimakin shugaban ƙasa sun dira Sakatariyar APC

Tsohon shugaban kasa Obasanjo.
Yanzun Nan: Gwamnonin Jam'iyyar PDP Uku Sun Saka Labule da Obasanjo Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Sun dira laburarin tsohon shugaban ƙasan OOPL da misalin ƙarfe 6:40 na yammacin yau Litinin tare da jerin gwanon motoci, ba ɓata lokaci suka shiga ganawar kai tsaye.

Gwamna Wike kuma ɗan takarar kujera lamba ɗaya a Najeriya ne ya jagorance su domin sanarwa da kuma neman goyon bayan Obasanjo game da burinsa na zama shugaban ƙasa.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Me suka tattauna a taron?

Da yake jawabi jim kaɗan bayan kammala tattaunawa da gwamnonin, Obasanjo ya tabbatar da cewa Wike ya gaya masa niyyarsa ta takara, amma ya masa fatan Alheri.

Obasanjo ya ayyana Najeriya a matsayin wata ƙasa mai ruɗani amma ba zata yi wahalar jagoranta ba matuƙar, "shugabanni masu kwarin guiwa," suka ci zaɓe.

Ya ce:

"Tabbas gwamna Wike a matsayin ɗan takarar shugaban kasa tare da gwamnan Oyo, gwamnan Benuwai, tsohon gwamnan Kuros Riba, tsohon mataimakin shugaban Sanatoci, da tsohon minista sun gana da ni kan burin takara."

Kara karanta wannan

Matsala ta kunno kai, Babban jigon APC ya sauya sheka zuwa PDP a Zamfara, ya tsaya takara 2023

"Kuma tabbas na ɗauki matsaya, ko da yaushe kan haka nike, na zaɓi zama masoyin siyasa, ni ba ɗan kowace jam'iyya bace amma idan siyace walwalar mutane ba zan so zama ɗan siyasa ba saboda kullum bukatata mutane su yi walwala."

A wani labarin kuma Buhari, Ministar mata da matar mataimakin shugaban ƙasa sun dira Sakatariyar APC

Matar shugaban ƙasa mace lamba ɗaya, Aisha Muhammadu Buhari, da matar Obasanjo sun ziyarci Sakatariyar APC ta ƙasa.

Manyan matan biyu tare da rakiyar Ministar harkokin matasa, Dame Pauline Tallen, sun gana da shugaban APC, Abdullahi Adamu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel