Shugaba Buhari ga Najeriya: Ba zan huta ba har sai an samu zaman lafiya a kasar nan
- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tabbatarwa 'yan Najeriya cewa, gwamnatinsa ba za ta ba 'yan Najeriya kunya ba
- Shugaban ya bayyana hakan ne yayin da ya kai ziyara jihar Kano domin halartar makon sojojin sama da aka gudanar
- Shugaban ya kuma bayyana cewa, gwamnatinsa ta zuba hannun jari mai yawa domin ganin an dakile matsalolin da suka shafi tsaro
Jihar Kano - Channels Tv ta ruwaito cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen kokarin dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar nan.
Buhari ya bayyana haka ne a ranar Litinin yayin bikin cika shekaru 58 da kafa rundunar sojojin saman Najeriya a Kano, TheCable ta ruwaito.
Shugaban ya ce zuba jarin da gwamnatinsa ta yi a rundunar sojin sama ya taimaka wajen karya lagwon 'yan ta'adda a kasar.
Ya yi alkawarin cewa, zai ci gaba da bai wa sojin sama goyon baya da ya dace a yaki da rashin tsaro da kasar ke fuskanta.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya kara da cewa:
“Zuba jarin da ake samu a rundunar sojojin saman Najeriya, ya taimaka wajen kawo karshen ta’addanci da ‘yan ta’adda a kasarmu.
“A ci gaba da yunkurinmu na ci gaba da kara yin aiki don tallafawa sojojin sama. Ka kwana da sanin cewa gwamnatinmu a shirye take ta kara himma wajen ganin an samar da tallafin da ake bukata da karfafa gwiwar shawo kan kalubalen tsaro daban-daban.
“Wannan gwamnati ba za ta huta ba har sai ta dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a cikin al’umma. Don haka ina kira gare ku da ku tsaya tsayin daka, ku jajirce tare da tilasta kansu wajen ganin zaman lafiya ya wadata a Najeriya.”
A watan da ya gabata, kungiyar dattawan Arewa (NEF) ta bukaci shugaban kasar da ya duba yiwuwar kawo zaman lafiya ko ya sauka cikin gaggawa.
Sai dai fadar shugaban kasar ta mayar da martani inda ta ce kiraye-kirayen yin murabus ba zai magance kalubalen tsaron da kasar ke fuskanta ba.
Ziyara gidan Sarkin Kano: Buhari ya gana da iyalan wadanda bam ya tashi dasu a Kano
A wani labarin, This Day ta rahoto cewa, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da ‘yan uwan wadanda suka mutu sakamakon fashewar nakiya da ya faru a Kano.
Shugaban wanda ya ziyarci Kano domin halartar taron makon sojojin saman Najeriya, ya gana da ‘yan uwan mutum 9 da suka rasu a fadar Sarkin Kano, inji rahoton Daily Trust.
Buhari ya jajanta wa iyalan da Sarki da gwamnatin jihar Kano kan wannan mummunan lamari, wanda ‘yan sanda suka ce fashewar iskar gas da wani sinadarai ne amma daga baya suka sauya batu.
Asali: Legit.ng