Dalibai sun shiga yanayi a wani bidiyo bayan Shugaban makaranta ya tattara kuɗin WAEC ya tsere
- Wani bidiyo da ya watsu a kafafen sada zumunta ya nuna yadda aka shanya wasu ɗalibai yayin da suka zo zana jarabawar WAEC
- Makasudin haka shi ne shugaban makaranta ya tattara kuɗin rijistar WAEC daga hannun ɗalibai kuma aka neme shi aka rasa
- Bidiyon ya yi bayanin cewa lamarin ya faru ne a jihar Edo kuma fusatattun ɗaliban sun rage fushinsu a kan Tagunan harabar makaranta
Edo - Wani shugaban makaranta wanda har yanzun ba'a gano bayanansa ba ya tattara kuɗin jarabawar fita daga Sakandire WAEC daga bisani aka neme shi aka rasa a jihar Edo.
A wani Bidiyo da ya watsu a kafafen sada zumunta wanda Legit.ng Hausa ta gani, shugaban makarantar bai yi wa ɗaliban da suka bashi kuɗi rijista ba, ya shanya su a ranar farko ta fara jarabawa.
A cikin Bidiyon an ga ɗaliban da ke ajin ƙarshe a babbar Sakandire wato SS 3, waɗan da ya dace ace suna cikin aji suna jarabawa, sun fusata suna aika-aika a harabar makarantar.
Rahotanni sun bayyana cewa mamallakin makarantar ya sa ta a kasuwa ƙamar yadda mutane suka ga an kafa allon sanarwa a babbar kofar shiga harabar wurin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An hangi ɗaliban suna jifan ginin makarantar da abubuwa daban-daban, suna farfasa tagogi kuma suna karya kayayyakin makaranta.
Duba Bidiyon anan.
Mutane sun yi martani a Istagram
@naomikamara92 ya ce:
"Abun ba dadi amma ya ba ni dariya sosai, ba na mamakin duk abin da mutanen mu na Benin suka yi ba domin za su iya mafi haka."
@Hypegad ya ce:
"Ƙannen mu sun rasa goben su dai a nan wurin, wannan abun tsoro ne."
@ngfabs ya ce:
"Shin wannan wasa ne? Wane kalan wasa ne wannan?"
@oluwa_soji7 ya ce:
"Ba abun kunyar da bazaka gani ba a kasar nan ta mu Najeriya duk ƙanƙantar shi."
@chigozie_ehim1 ya yi martani da cewa:
"Kamata ya yi a kama shi cikin gaggawa."
A wani labarin kuma Fusatattun Mutane sun yi ajalin wani dan fashi ɗa dubunsa ta cika a jahar Katsina
Mutane sun yi ajalin mutum ɗaya daga cikin tawagar yan fashi da dubunsu ta cika a karamar hukumar Charanchi ta jihar Katsina.
Bayanai sun nuna cewa yan sanda sun kai ɗauki dan kama yan fashin bayan sun kwace motar wani Abdulmumini a gona.
Asali: Legit.ng