Sarkin Katsina ga Osinbajo: Muna bayanka, Ina addu'ar ka yi nasarar gaje Buhari
- Alhaji Abdulmumin Usman, Sarki Katsina, ya bayyana cewa yana goyon bayan Farfesa Osinbajo a yunkurinsa na son gaje kujerar Buhari
- A cewar basaraken, yana masa addu'a ya yi nasara kuma ya dasa daga inda Buhari ya tsaya duba da irin gogewar da Osinbajo ke da ita
- A bangaren mataimakin shugaban kasar, ya bayyana cewa ya san matsalolin Najeriya kuma zai iya shawo kansu matukar ya haye madafun iko
Katsina - Abdulmumin Usman, Sarkin Katsina, ya ce yana goyon bayan takarar da mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo da yake yi domin gaje kujerar ubangidansa Buhari.
Usman ya sanar da hakan ne yayin da osinbajo ya ziyarcesa a fadarsa da ke Katsina a ranar Asabar, The Cable ta ruwaito.
Basaraken gargajiyan ya ce mataimakin shugaban kasan zai iya mulkar kasar nan.
"Ka ji daga gare ni, muna bayan ka; za mu yi iyakar kokarinmu; mutum mai gogewa ya fi wanda zai zamana sabo ga tsarin mulkin; don haka kana gaba." Premium Times ta bayyana a cewarsa.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Kana bukatar wasu karin armashi, karin armashin da kake bukata kuwa su ne shawarwari. Mu ne tushen, ka shawarci masarautun gargajiya, ka yi tafiyar tare da su.
“Ina yi maka addu'a ka samu nasara, ka dasa daga inda wanda ya gabace ka ya tsaya kuma Allah zai taimake ka.
“Na san cewa kai mutum ne mara hayaniya, fasto, ka san Ubangiji, ka san yadda za ka tafi da shi, za mu yi maka addu'a da izinin Allah, amma ka sanya a zuciyarka cewa wannan aiki ne da dole a yi shi."
Mene ne martanin Osinbajo?
A bangarensa, Osinbajo ya ce wannan matsayin da yake kai da kuma zamansa mukaddashi shugaban kasar Najeriya kadai ya gogar da shi ta yadda zai mulki kasar.
"Na kawo kaina domin neman kujerar shugabancin kasar Najeriya kuma in gaji shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda zai sauka daga kujerar a ranar 29 ga watan Mayun 2023 da izinin Ubangiji," yace.
"Na mika kaina ne saboda ganin cewa na yi aiki karkashin koyarwarsa a shekaru bakwai da suka gabata kuma wasu lokutan na zama mukaddashin shugaban kasa.
"A wannan lokacin, shugaban kasan ya nuna min abubuwan da ya kamata in sani game da mulki a kasa irin tamu.
“Ina so in sanar da ku cewa na koya; ina da gogewa kuma manyan abubuwan da kasar nan ke bukata su ne tsaro, tattalin arziki wanda na yadda cewa zan iya shawo kansu."
Shugaban kasa a 2023: Osinbajo na kamun kafa da sarakuna
A wani labari na daban, mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, ya nemi goyon bayan majalisar sarakunan gargajiya a jihar Cross River a kokarinsa na son zama shugaban kasa a karkashin inuwar jam’iyyar All Progressives Congress (APC).
Osinbajo wanda ya ziyarci majalisar sarakunan a ranar Alhamis, 5 ga watan Mayu a Calabar, ya ce sarakunan gargajiya wadanda sune suka fi kusa da mutane, suna taka muhimmiyar rawar gani a ci gaban kasar, Daily Trust ta rahoto.
Ya fada masu cewa kasanvcewar ya yi aiki a matsayin mataimakin shugaban kasa tsawon shekaru bakwai yana da tarin gogewa domin jagorantar kasar a matsayin shugaban kasa.
Asali: Legit.ng