Kiristocin CAN: Ana amfani da sunan zagin Annabi domin kashe Kiristoci a Arewa

Kiristocin CAN: Ana amfani da sunan zagin Annabi domin kashe Kiristoci a Arewa

  • Kungiyar CAN ta yi babban tsokaci game da rikicin da ya kunno kai a Arewacin Najeriya na batanci ga AnnabiKungiyar CAN ta yi babban tsokaci game da rikicin da ya kunno kai a Arewacin Najeriya na batanci ga Annabi
  • Kungiyar ta ce tana zargin musulmi da kitsa sabuwar hanyar kashe kirista ba tare da wata hujja mai karfi ba
  • Hakazalika, ta yi kira ga hukumomin gwamnati da su dauki matakin gaggawa kan irin wannan matsala ta Arewa

Kungiyar kiristoci ta Najeriya CAN a karshen mako ta zargi cewa zarge-zargen batanci na zama wata sabuwar hanyar kashe Kiristoci musamman a Arewa.

Ta ce zarge-zargen karya ne kuma kawai ana yi ne don kashe abokan gaba ko kuma 'yan mata masu kamun kai da suka ki aikata lalata da wadanda ba Kirista ba, The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Cikin katatafaren kadarorin da suka tsunduma AGF Ahmed Idris a komar EFCC

Kungiyar kiristocin ta yi kira ga hukumomin gwamnati da jami’an tsaro da su yi gaggawar magance matsalolin kafin su haifar da rikici mai tsanani da ba za a iya magancewa ba.

Rikici a Bauchi saboda yunkurin kashewata mata da ake zargin ta zagi annabi
CAN: Ana amfani da sunan zagin Annabi domin kashe Kiristoci a Arewa | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: UGC

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Mataimakin shugaban kungiyar ta CAN, (jihohin Arewa 19 da Abuja), Rabaran Joseph John Hayab ne ya bayyana haka a Abuja yayin da yake mayar da martani game da rikicin da ya barke a yankin Katangan da ke karamar hukumar Warji ta jihar Bauchi.

Idan baku manta ba, an samu rahotannin da ke bayyana yadda wasu ke neman wata matar da ake zargi ta yi ga Manzon Allah SAW a wani yankin jihar Bauchi.

Lamarin da ya faru a Bauchi ya zo ne makwanni biyu bayan kisan wata daliba taa Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari da ke Sakkwato, Deborah Emmanuel kan zagin Annabi Muhammad SAW.

Kara karanta wannan

Jihar Bauchi: Gwamna ya yi martani kan zagin Annabi da wata mata ta yi

Batanci ga Annabi: Gwamnati ta cire takunkumi a Sokoto, ta haramta zanga-zanga

A wani labarin, gwamnan jihar Sokoto, Aminu Tambuwal, a ranar Juma'a, ya dage dokar hana fita da aka kafa a birnin Sokoto, sakamakon rikicin da ya biyo bayan kisan Deborah Samuel.

Gwamnan ya kuma haramta duk wani nau'in zanga-zanga da gangami a fadin a jihar har sai baba-ta-gani, Channels Tv ta ruwaito.

Rahotanni a baya sun ce, wasu fusatattu sun lallasa Deborah Samuel, dalibar Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari, bisa zarginta da dura ashariya ga manzon Allah SAW.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.