Bayan fille kan ‘Dan Majalisa da sace wani dan siyasa, ‘Yan bindiga sun ce 'za su dawo'
- Wadanda ake zargi da hannu wajen kashe Okechukwu Okoye sun yi barazanar cigaba da yin ta’adi
- A karshen makon da ya wuce ne aka tsinci kan ‘dan majalisar Aguata II, Hon, Okechukwu Okoye
- Mutanen gari sun tsinci wata takarda da ta ce ‘yan bindigan za su cigaba da kashe ‘yan majalisa
ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit
Anambra - Yayin da al’ummar garin Aguata su ke makokin mutuwar Okechukwu Okoye, sai aka ji wani labari wanda ya fi na kisan da aka yi masa firgici.
Daily Trust ta rahoto cewa miyagun ‘yan bindigan da ake zargi da laifin kashe Hon. Okechukwu Okoye, sun ce za su cigaba da kashe wasu ‘yan majalisan.
A ranar Asabar aka tsinci kan Okoye a Nnobi a yankin Idemili, bayan wadannan ‘yan bindigan sun hallaka ‘dan majalisan jihar da su ka yi garkuwa da shi.
Wani mazaunin garin Nnobi ya shaidawa jaridar cewa wadanda suka yi wannan danyen aiki sun bar wata takardar barazana a gefen kan da suka jefar a titi.
Sahara Reporters ta bayyana cewa takardar da aka bari dauke da kan da aka datse ta na barazanar mutanen za su cigaba da kashe ire-iren Hon. Okoye.
“A takardar, makasan sun yi alkawarin cewa za a zubar da wasu kawunan. Ba a fahimci abin da takardar da kunsa sosai ba.”
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Ruwan sama ya bata takardar da aka bari, amma ta fara ne da kalamar da ke nuna ‘gargadi’.”
“A cikin takardar, an rubuta cewa, ‘duk inda ku ka je, ba za ku iya boyewa a ko ina ba. Za mu bi ku duk daya bayan daya...”
“...Domin jami’an ‘yan sanda da dakarun sojojin kasa ba matsalar mu ba ne kuma a yanzu.”
'Batanci: Ba Za Mu Lamunci Kashe Kiristoci a Bauchi Ba Da Sunan Zagin Annabi, CAN Ta Ja Kunnen Musulmi
Ana zargin cewa ‘yan bindiga sun tare a yankunan Unubi da ke karamar hukumar Nnewi. Daga nan ne suka kai hari, su na kashe mutane a yankunan Anambra.
Sa’o’i kadan bayan hakan sai aka ji cewa ‘yan bindiga sun dauke wani ‘dan siyasa a Nnewi, Uzozie Chukwujekwu har sun harbe yaronsa daya da ya mallaka a Duniya.
Rikici a zabukan PDP
Ku na da labari cewa tun karfe 10:00 ya kamata a fara zaben tsaida ‘dan takaran majalisa, amma har zuwa karfe 6:45 ana rigima tsakanin ‘ya ‘yan PDP a wasu jihohi.
Rotimi George Taylor mai neman takarar ‘dan majalisa a jihar Ogun ya ce an yi awon-gaba da masu kada kuri’a, amma jam’iyyar PDP ta karyata wannan maganar.
Asali: Legit.ng