Miyagun yan bindiga sun kashe uwa da 'ya'yanta hudu, sun haɗa da wasu mutum 2 a Anambra
- Yan bindiga sun kai hari garuruwa daban-daban a jahar Anambra, aƙalla mutum Bakwai ne suka rasa rayukan su
- Wasu shaidun gani da ido sun bayyana cewa maharan sun shiga yankunan da abun ya shafa suka buɗe wa mamatan wuta
- Kakakin rundunar yan sanda na jihar Anambra ya ce hukumar zata fitar da sanarwa ranar Litinin bayan ta tattara bayanai
Anambra - Miyagun yan bindiga sun halaka aƙalla rayuka Bakwai a sassa daban-daban na jahar Anambra, kamar yadda The Nation ta ruwaito.
Daga cikin su har da wata mahaifiya tare da ƴaƴanta huɗu, waɗan da suka rasa rayukansu a Isulo, ƙaramar hukumar Orumba ta arewa.
Sauran mutum biyun kuma sun yi bankwana da duniya ne a ƙauyen Abatete, ƙaramar hukumar Idemili ta arewa yayin da aka kashe wani mutum ɗaya Nanka, Orumba ta arewa.
Wasu shaidun da suka gani da idanun su, sun shaida wa jaridar cewa yan bindigan yan bindigan sun shiga waɗan nan yankunan suka buɗe wa mutanen wuta, daga bisani suks fece.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ba mu da cikakken bayani - Yan sanda
Kakakin hukumar yan sanda reshen jihar Anambra, Ikenga Tochukwu, ya ce ba zai iya tabbatar da faruwar lamarin ba saboda ba bu cikakken bayani kan ta'asar da maharan suka yi.
Ya ce hukumar yan sanda zata fitar da jawabi kan abin da ya faru ranar Litinin, lokacin sun samu cikakken bayani kan duk abin da ya faru, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Sai dai wani babban jami'i a hukumar yan sanda, wanda ya nemi a sakaya bayanan sa, ya gaya wa manema labarai cewa harin Isulo ya faru dagaske.
Yanzu-yanzu: Buhari ya nada sabon mukaddashi Akanta Janar, ya maye gurbin Ahmed Idris dake hannun EFCC
A wani labarin kuma CAN ta canza salon zanga-zangar da kiristoci zasu yi yau kan kashe wacce ta zagi Annabi a Sokoto
Kungiyar kiristoci ta ƙasa CAN ta sake fitar da wata sanarwa game da zanga-zangar da ta shirya gudanarwa yau kan kisan Deborah a Sokoto.
A sanarwar, shugaban CAN na ƙasa ya umarci shugabannin Coci-Coci su canza salo , sun gano akwai wata maƙarkashiya.
Asali: Legit.ng