CAN ta canza salon zanga-zangar da kiristoci zasu yi yau kan kashe wacce ta zagi Annabi a Sokoto

CAN ta canza salon zanga-zangar da kiristoci zasu yi yau kan kashe wacce ta zagi Annabi a Sokoto

  • Kungiyar kiristoci ta ƙasa CAN ta sake fitar da wata sanarwa game da zanga-zangar da ta shirya gudanarwa yau kan kisan Deborah a Sokoto
  • A sanarwar, shugaban CAN na ƙasa ya umarci shugabannin Coci-Coci su canza salo, sun gano akwai wata maƙarkashiya
  • CAN ta umarci a gudanar da shirin yau Lahadi kamar yadda ta tsara amma a harabar Coci, idan hakan ba ta samu ba a yi cikin Coci

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Ƙungiyar kiristoci ta ƙasa (CAN) ta bukaci kiristoci su canza dabarar zang-zangar kashe Deborah Samuel a Sakkwato bisa zargin ta zagi Annabi SAW a Sokoto.

Shugaban CAN na ƙasa, Dakta Samson Olasupo Ayokunle, shi ne ya sanar da sabon canjin a wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Zagin Annabi: Dole A Yi Adalci Kan Kisar Deborah Yakubu, In Ji Amina Mohammed

Kungiyar CAN ta canza salo.
CAN ta canza salon zanga-zangar da kiristoci zasu yi yau kan kashe wacce ta zagi Annabi a Sokoto Hoto: dailytrust.com
Asali: Twitter

Ya umarci dukkanin shugabannin Coci Coci da wuraren ibadar mabiya addinin Kirista da su gudanar da zanga-zangar lumana a cikin Cocin su a yau Lahadi, 22 ga watan Mayu, 2022.

Sanarwan ta ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Duk kuna da masaniyar cewa wasu Musulmai sun fitar da bayanan zasu kalubalanci zanga-zangar lumana da muka shirya ranar Lahadi 22 ga Mayu."
"Manufar su shi ne su tada zaune tsaye kuma su jingina mana laifin, saboda haka ina rokon ku baki ɗaya ku yi zanga-zanga ɗauke da alluna a ciki harabar Coci Cocin ku ko Sakatariyar CAN."
"Idan hakan ba ta samu ba, ku yi a cikin Coci ku ɗaga alluna ku yi Addu'a a yi wa Deborah Samuel Adalci. Ku yi Addu'a Allah ya canza zuciyar wanda ke da nufin kashe mutum ɗan uwansa da rigar addini."

Ku yaɗa wa duniya ta kafafen sada zumunta - CAN

Kara karanta wannan

Batanci ga Annabi: Gwamnati ta cire takunkumi a Sokoto, ta haramta zanga-zanga

Shugaban CAN ya kuma ya umarci shugabannin Coci Coci da su bar yan jarida da kafafen talabijin su ɗauƙi zanga-zangar lumana ta cikin gida.

Haka nan kuma ya bukaci su yi amfani da kafafen sada zumunta, su ɗauki hotuna su watsa domin duniya ta sani.

A wani labarin kuma Gwamna Ortom ya yaba wa ɗan takarar APC, ya ce ya cancanci ya gaji Buhari a 2023

Gwamna Samuel Ortom na Benuwai ya ce shugaban NGF kuma gwamnan Ekiti, Kayode Fayemi, ya cancanta ya mulki Najeriya.

Ortom na jam'iyyar PDP ya yaba wa ɗan takarar shugaban ƙasa na APC ne yayin da ya karɓi bakuncinsa a fadar gwamnati ranar Asabar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel