Zagin Annabi: Soyinka Ya Ce Dole a Sauke Maqari Daga Limanci a Abuja Soboda Ya Goyi Bayan Kashe Deborah

Zagin Annabi: Soyinka Ya Ce Dole a Sauke Maqari Daga Limanci a Abuja Soboda Ya Goyi Bayan Kashe Deborah

  • Farfesa Wole Soyinka, ya ce dole a sauke limamin babban masallacin kasa na Abuja Farfesa Ibrahim Maqari daga mukaminsa saboda tunzura mabiyansa
  • Soyinka ya zargi Maqari da umurtar mabiyansa su dauki doka a hannunsu da sunan addini saboda goyon bayan kashe Deborah Yakubu da limamin ya yi inda ya ce ta aikata babban laifi na zagin Annabi SAW
  • Marubucin wanda ya taba lashe kyautar Nobel ya yi wannan jawabin ne a birnin tarayya Abuja a ranar Asabar wurin taron kaddamar da littafi kan tarihin marigayi Laftanar Janar Ibrahim Attahiru

Abuja - Fitaccen marubuci wanda ya taba lashe kyautar Nobel, Farfesa Wole Soyinka, ya yi kira da a sauke limamin babban masallacin kasa na Abuja, Farfesa Ibrahim Maqari, daga mukaminsa kan kalaman da ya furta game da kisar Deborah Yakubu, dalibar Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari a Sokoto saboda zagin Annabi (SAW).

Kara karanta wannan

Yan kasar Nijar, da wasu yan bakin haure ke aikin Okada a Legas, Kwamishanan yan sanda

The Punch ta rahoto cewa Soyinka ya zargi limamin da umurtar mabiyansa su dauki doka a hannunsu da sunan addini.

Zagin Annabi: Soyinka Ya Buƙaci a Sauke Maqari Daga Limanci a Masallacin Ƙasa a Abuja
Soyinka Ya Buƙaci a Cire Maqari Daga Limanci a Masallacin Ƙasa a Abuja. Hoto: The Punch.
Asali: Twitter

Ya yi wannan jawabin ne a ranar Asabar a Abuja yayin taron shekara guda da rasuwar tsohon babban hafsan sojojin kasa na Najeriya, Laftanar Janar Ibrahim Attahiru da kaddamar da littafin tarihinsa da marubuci Niran Adedokun ya rubuta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya zama dole a tsige Farfesa Maqari daga limanci - Farfesa Soyinka

Soyinka ya nuna rashin jin dadinsa game da kisa da sunan addini, ya kara da cewa 'Ya zama dole a cire wanda ya kauracewa tsarin mutuntaka, Farfesa Maqari.'

Ya kara da cewa:

"Ba za mu lamunci musulmi su rika fakewa da cewa musulunci ya ce kaza da kaza ba, ko Sharia kaza da kaza ne, ko kuma Annabi Mohammed (SAW) ya yi misali iri kaza ko ya furta magana na jin kai iri kaza.

Kara karanta wannan

Bayan Kwana Uku a Tsare, EFCC Ta Sako Tsohuwar Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya

"Mun wuce matakin da za a rika magana a fatan baki kawai na halayen mutuntaka, ya kamata a aikata abin da ake fada."

A ruwayar ta The Punch, marubucin wasannin kwaikwayon ya ce malamin na addinin musulunci ba komai ya yi ba illa karfafawa mabiyansa gwiwa su kashe duk wani da ya yi batanci ga Annabi Muhammad (SAW).

Ya cigaba da cewa:

"Farfesa Maqari da wasu tsiraru, ciki har da yan sanda a baya-bayan nan ba su nuna nadama ba bisa azabtarwa da kashe dalibar a duniyan nan.
"Maqari a kaikaice ya umurci mabiyansa su dauki doka a hannunsu da sunan addini. Wannan shine sakon malamin addinin ga kasar da ke fuskantar abubuwa na rashin hankali."

Wata Mata Ta Sake Zagin Annabi a Bauchi, Matasa Sun Bazama Nemanta, Sun Kona Gidaje Sun Raunata Fasto

A wani rahoton, kun ji cewa ana zaman dar-dar a Bauchi sakamakon zargin furta kalaman batanci ga Annabi (SAW) da wata Mrs Roda Jatau ta yi, wanda aka yada a wani dandalin Whatsapp, rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Gwamnatin tarayya ta dakatad da dawowa aikin jirgin kasa Abuja-Kaduna sai baba ta gani

A cewar majiyar, Mrs Jatau ma'aikaciya ce a Hukumar Lafiya Bai Daya ta Jihar Bauchi kuma asalin ta yar Gombe ne amma ta auri wani dan karamar hukumar Warji.

Rahotanni sun nuna cewa matasa musulmi sun bazama nemen matar bayan sallar Juma'a amma ba su ganta ba domin an tsere da ita, rahoton The Punch.

Asali: Legit.ng

Online view pixel