Gwamnatin tarayya ta dakatad da dawowa aikin jirgin kasa Abuja-Kaduna sai baba ta gani

Gwamnatin tarayya ta dakatad da dawowa aikin jirgin kasa Abuja-Kaduna sai baba ta gani

  • Ana saura kwanaki biyu a dawo aiki, hukumar jiragen kasa ta bayyana cewa ta dage dawowa jigilar fasinjoji
  • Tuni dai iyalan wadanda yan bindiga suka sace a jirgin kasan sun bayyana cewa ba zasu yarda jirgin ya cigaba da aiki ba
  • Yan bindiga sun kai hari jirgin kasan Abuja-Kaduna ne ana saura yan kwanaki azumin Ramadana, har yanzu mutum uku kadai suka saki cikin kimanin 70

Legas - Hukumar jiragen kasan Najeriya NRC ta dakatar da dawowar jirgin kasan dake jigilar fasinjoji tsakanin Abuja da Kaduna sai wani lokaci da ba'a sani ba.

Wannan ya biyo bayan lashe takobin da iyalan wadanda aka sace a jirgin kwanaki suka yi na cewa ba zasu amince jirgin ya dawo aiki ba sai an dawo yan'uwansu da aka sace.

Kakakin hukumar NRC, Mr. Mahmud Yakub, a jawabin da ya fitar ranar Juma'a ya bayyana cewa za'a sanar da sabon ranar dawowar jirgin.

Kara karanta wannan

Cikin katatafaren kadarorin da suka tsunduma AGF Ahmed Idris a komar EFCC

Yace:

"Hukumar NRC zata cigaba da bada hadin kai da gwamnatin tarayya wajen kare rayukan mutanen Najeriya da dukiyoyinsu."
"Hakazalika muna jajantawa iyalan wadanda ke hannun yan bindiga har yanzu sakamakon harin da aka kai jirgi kuma muna tabbatar muku gwamnatin tarayya na kokarin ceto dukkan wadanda ke tsare."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jirgn kasa
Gwamnatin tarayya ta dakatad da dawowa aikin jirgin kasa Abuja-Kaduna sai baba ta gani

Titin Abuja-Kaduna: El-Rufa'i ya bada shawarar tayar da wasu garuruwa uku dake kan hanyar

Gwamnan jihar Kaduna,Nasir El-Rufai, a ranar Alhamis ya bada shawaran tayar da kauyukan Katari, Rijana da Akilibu, dake kan titin babbar hanyar Kaduna-Abuja.

Yace masu kaiwa yan bindiga bayanai ne suka cika wadannan kauyuka.

El-Rufa'i ya bayyana hakan ne yayin karban rahoton irin hare-haren yan bindigan da jihar Kaduna ta fuskanta tsakanin watar Junairu da Maris, rahoton TheNation.

Ya ce yanzu yan ta'adda sun tashi daga Arewa maso gabas, sun shiga Arewa maso yamma.

Asali: Legit.ng

Online view pixel