Kano: Ƴan Sanda Sun Kama Mota Maƙare Da Kayan Haɗa Bamai-Bamai Da Bindigu

Kano: Ƴan Sanda Sun Kama Mota Maƙare Da Kayan Haɗa Bamai-Bamai Da Bindigu

  • Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano ta kama wata mota cike taf da abubuwan hada bama-bamai da bindigogi guda biyu kirar AK-47
  • Kakakin rundunar na Jihar Kano, Abdullahi Kiyawa ya bayyana hakan inda ya ce an kama motar ne bayan sun samu bayanan sirri akai
  • A cewarsa, wanda ya tuka motar ya sake ta a Bubbugaje Quarters da ke karamar hukumar Kumbotso yayin da ya yi gaggawar tserewa

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Jihar Kano - Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano ta yi nasarar yin ram da wata mota cike makil da abubuwan hada bama-bamai da bindigogi kirar AK-47, Daily Nigerian ta ruwaito.

Kamar yadda kakakin rundunar na Jihar Kano, Abdullahi Kiyawa ya bayyana a wata takarda, ya ce bayan samun bayanan sirri ne su ka bi sawun motar.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Wata Mata Ta Sake Zagin Annabi a Bauchi, Matasa Sun Bazama Nemanta, Sun Ƙona Gidaje Sun Raunta Fasto

Kano: Ƴan Sanda Sun Kama Mota Maƙare Da Kayan Haɗa Bamai-Bamai Da Bindigu
'Yan Sanda Sun Kama Mota Maƙare Da Kayan Haɗa Bamai-Bamai Da Bindigu a Kano. Hoto: Daily Nigerian.
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Har da bindigogi da harsasai a cikin motar

A cewarsa kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito:

“A ranar 19 ga watan Mayun 2022, mu ka samu bayanan sirri akan cewa ana zargin wata mota kirar Mercedes Benz ma kalar ruwan toka cike ta ke abubuwa masu fashewa (IEDs) kuma ta taho ne daga Jihar Jigawa zuwa Jihar Kano.
“Kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Sama’ila Shu’aibu Dikko, ya yi gaggawar tura jami’ai ciki har da Explosive Ordnance Disposal-Chemical, Biological, Radiological and Nuclear Defence (EOD-CBRN) da Operation Puff Adder.
“Da misalin karfe 4 da rabi na yamman ranar bayan bin motar na tsawo lokaci, daga bisani wanda ake zargin ya yada motar a Bubbugaje Quarters da ke karamar hukumar Kumbotso a Jihar Kano ya tsere.”

Ya ci gaba da shaida yadda bayan yin binciken fasaha aka gano cewa motar cike ta ke abubuwan hada bama-bamai, bindigogi kirar AK-47 guda biyu, magazin na AK-47 guda hudu, harsasai masu rai guda 1,098 da kananun bindigogi guda biyu.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Hatsarin mota ya rutsa da dan takarar gwamnan APC a Abuja

Takardar ta bayyana cewa har yanzu ana ci gaba da bincike akan lamarin.

'Yan Sanda Sun Cafke Matashin Da Ke Kai Wa 'Yan Bindigan Neja Abinci

A wani rahoton, Rundunar ‘yan sandan Jihar Neja ta kama wani matashi mai shekaru 20, Umar Dauda wanda ake zargin yana kai wa ‘yan ta’adda kayan abinci a jihar, The Punch ta ruwaito.

A wata takarda wacce jami’in hulda da jama’an rundunar ‘yan sandan jihar, Wasiu Abiodun ya sanya wa hannu, an samu bayani akan yadda aka kama matashin bayan mazauna yankin sun bayar da bayanan sirri ga hukuma.

Kamar yadda takardar tazo:

“An yi kamen ne a ranar 16 ga watan Maris din 2022, da misalin karfe 11 na dare bayan samun bayanan sirri akan yadda ake yawan ganin wani mai kai wa ‘yan ta’adda kayan abinci a kauyen Kapako da ke Lapai.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel