Wata Mata Ta Sake Zagin Annabi a Bauchi, Matasa Sun Bazama Nemanta, Sun Kona Gidaje Sun Raunta Fasto
- Hankula sun tashi a Bauchi yayin da ake zargin wata Roda Jatau, wacce ta yi ridda da batanci bayan ta saki wani bidiyo a WhatsApp tana sukar Annabi
- Kamar yadda majiyar ta bayyana, Jatau ma’aikaciyar asibiti ce a Jihar Bauchi amma asalin ‘yar Jihar Gombe ce kuma aure ne ya kai ta karamar hukumar Warji
- Rahotanni sun nuna yadda wasu matasan musulmai su ka bazama neman matar bayan sallar Juma’a amma ba su ganta ba saboda ta boye daga nan su ka tayar da tarzoma
Jihar Bauchi - Ana zaman dar-dar a Bauchi sakamakon zargin furta kalaman batanci ga Annabi (SAW) da wata Mrs Roda Jatau ta yi, wanda aka yada a wani dandalin Whatsapp, rahoton Vanguard.
A cewar majiyar, Mrs Jatau ma'aikaciya ce a Hukumar Lafiya Bai Daya ta Jihar Bauchi kuma asalin ta yar Gombe ne amma ta auri wani dan karamar hukumar Warji.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Rahotanni sun nuna cewa matasa musulmi sun bazama nemen matar bayan sallar Juma'a amma ba su ganta ba domin an tsere da ita, rahoton The Punch.
Matasa sun raunana kiristocin yankin da dama
Kawo yanzu, matasan musulmai sun lalata abubuwa da dama da kiristocin yankin su ka mallaka sannan sun kona gidaje da yawa.
Wakilin Punch ya bayyana yadda wata majiya ta shaida masa cewa:
“Abinda na fahimta shi ne yadda wata kirista ta yi tsokaci akan lamarin da ya faru a Sokoto a makon da ya gabata a kafar sada zumunta, daga nan ne rikicin ya samu asali.
“Duk da dai babu wanda aka halaka har yanzu amma dai an kona gidaje sannan an yi asarar dukiyoyi da dama.”
Vanguard ta tattaro cewa an raunana kiristoci da dama har da faston cocin ECWA.
Shugaban Kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) na reshen jihar ya ce ya sanar da Kwamishinan ‘yan sanda da kuma Babban Hadimin Gwamna Bala Mohammed na Musamman akan wannan lamarin.
Kwanaki kadan kenan da halaka Deborah Samuel
Ya kuma yi kira ga Kiristocin yankin cewa kada su bari wannan lamarin ya razana su, duk da dai ya kamata su dage wurin kare kawunansu.
Har lokacin rubuta rahoton nan, ‘yan sanda ba su riga sun saki wata takarda ba dangane da rikicin.
Wannan ya biyo bayan kwanaki kadan da abokan karatun wata dalibar Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari a Sokoto, Deborah Samuel, su ka halaka ta sannan su ka kona gawarta akan zarginta da batanci ga Annabi.
Zagin Annabi: Dole A Yi Adalci Kan Kisar Deborah Yakubu, In Ji Amina Mohammed
A wani rahoto, Mataimakiyar Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, UN, Amina Mohammed, ta ce ya zama dole a yi adalci game da kashe Deborah Samuel Yakubu, wacce aka halaka sannan aka kona a Sokoto.
Mohammed, wacce ta yi wannan kirar a cikin wani wallafa da ta yi a shafinta na Twitter a ranar Talata ta ce, bai dace a rika 'yi wa addini fasarar da bai dace ba domin tada rikici.'
Asali: Legit.ng