Da Dumi-Dumi: Yan bindiga sun sace shugaban ƙaramar hukuma da hadiminsa
- Wasu miyagu sun kashe ɗan sanda yayin da suka sace shugaban ƙaramar hukumar Keffi, Muhamamd Shehu, da direbansa a jihar Nasarawa
- Rahoto ya bayyana cewa maharan sun buɗe wa motarsa wuta yayin da ya kusa shiga Gudi, mahaifar gwamna Abdullahi Sule
- Kakakin hukumar yan sanda na jihar Nasarawa, ASP Ramhan Ramhan, ya tabbatar da faruwar lamarin ga yan jarida
Nasarawa - Miyagun yan bindiga sun sace shugaban ƙaramar hukumar Keffi a jihar Nasarawa, Honorabul Muhammad Baba Shehu, da kuma direbansa.
Jaridar The Nation ta rahoto cewa yan bindigan sun halaka dakaren ɗan sanda da ke tsare Ciyaman din, Sajan Alhassan Habibu Nasir.
Bayanai sun nuna cewa lamarin ya auku ne da misalin ƙarfe 6:30 na yammacin ranar Jumu'a a yankin Gudi, ƙaramar hukumar Akwanga ta jihar Nasarawa.
Dogarin shugaban ƙasarmar hukumar ya rasa ransa a hannun maharan ne yayin da suka yi musayar wuta, nan take a wurin Allah ya karɓi rayuwarsa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda lamarin ya faru
Ciyaman ɗin ya halarci babban taron shekara-shakara na kungiyar tsofaffin ɗaliban yankin Keffi (KOBA), inda jim kaɗan bayan kammala jawabi ya nemi uzurin cewa zai kama hanyar zuwa Lafia.
Rahoto ya bayyana cewa yan bindigan sun buɗe wa Motarsa wuta yayin da ya kusa Gudi, suka kashe dogarin ɗan sandan da suke tare, daga bisani suka yi gaba da shi da kuma direbansa.
Garin Gudi nan ne mahaifar gwamnan jihar Nasarawa, Gwamna Abdullahi Sule, na jam'iyyar APC.
Mai magana da yawun rundunar yan sanda reshen jihar Nasarawa, ASP Ramhan Ramhan, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai.
A wani labarin na daban kuma Gwamnan Arewa ya faɗi sunan ɗan takarar da zasu zaɓa a zaɓen fidda magajin Buhari na APC
Gwamnan jihar Filato, Simon Lalong, ya ce baki ɗaya Deleget ɗin jihar tsohon ministan Sufuri zasu kaɗa wa kuri'un su..
Lalong yace mutanen jihar Filato da shi karan kansa ba zasu taba mancewa da abin da ɗan takarar shugaban ƙasan ya musu ba.
Asali: Legit.ng