An Gurfanar Da Wani a Kotu Kan Wawushe Albashin 'Yan N-POWER Na Watanni Masu Yawa

An Gurfanar Da Wani a Kotu Kan Wawushe Albashin 'Yan N-POWER Na Watanni Masu Yawa

  • Wata babbar kotun majistare da ke Ado-Ekiti ta bayar da umarnin kama wani Baderinwa Waheed, mai shekaru 33 akan satar albashin N-Power din wata na watanni biyar
  • Kamar yadda mai gabatar kara, Mr Olaolu Olayinka ya bayyana, wanda ake zargin ya aikata laifin ne a watan Maris din 2021 a Ado-Ekiti
  • Olayinka ya yi zargin mutumin ya hada kai da wani Tiamiyu Salimot wurin amfani da na’ura mai kwakwalwa wurin shiga shafin N-Power din Adeola Olofin wurin damfararta

Ekiti - Bederinwa Waheed mai shekaru 33 ya gurfana gaban babbar kotun Majistaren Ado Ekiti bisa zarginsa da ake yi da damfarar wata albashinta na watanni biyar na N-Power.

The Nation ta ruwaito ana zargin mutumin wanda ba a bayyana adireshinsa ba da sata, damfara da sauran laifuka.

Kara karanta wannan

Batanci ga Annabi: Gwamnati ta cire takunkumi a Sokoto, ta haramta zanga-zanga

An Gurfanar Da Wani a Kotu Kan Wawushe Albashin 'Yan N-POWER Na Watanni Masu Yawa
An Gurfanar Da Wani a Kotu Kan Sace Albashin 'Yan N-POWER Na Watanni Masu Yawa. Hoto: The Guardian.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kamar yadda mai gabatar kara, Olaolu Olayinka ta bayyana, wanda ake zargi ya aikata laifin ne a watan Maris din 2021 a Ado-Ekiti.

Ana zarginsa da damfarar N150,000

Olayinka ya zarge shi da hada kai da Tiamiyu Salimot wurin amfani da na’ura mai kwakwalwa wurin shiga shafin N-power din Adeola Olofin don damfararta.

The Vangaurd ta ruwaito yadda ake zargin Waheed da Solimat da sauya suna, lambar asusun banki da kalaman sirrin Olofin, wanda hakan ya ja mata asarar albashin N-Power dinta na watanni biyar, N150,000.

Mai gabatar da kara ya ce wayarta ta samu matsala ne, wanda hakan ya sa ta gabatar masa da bayananta don ya duba mata sakwanni.

An sakaya wanda ake zargi

A cewarsa, wanda ake zargin ya nuna cewa babu wani sako da aka tura mata, daga nan ya koma amfani da bayananta kuma ya karkatar da kudin zuwa asusunsa har na tsawon watanni biyar.

Kara karanta wannan

2023: Bayan siyan fom din APC na N50m, dan takarar gwamna daga wata jihar Arewa ya sauya sheka

Olayinka ya ce, laifin ya ci karo da sashi na 14(1), (2) da (3) na laifukan yanar gizo na shekarar 2015.

Ba a amince da rokon da wanda aka gurfanar ya yi ba don haka Alkalin kotun, Mr Bankole Oluwasanmi, ya bayar da umarnin a sakaya shi har sai an ji abinda darektan ofishin hukunci na gwamnatin jihar ya tanadar.

Daga nan ya dage sauraron karar zuwa ranar 20 ga watan Yuni.

Asali: Legit.ng

Online view pixel