Titin Abuja-Kaduna: El-Rufa'i ya bada shawarar tayar da wasu garuruwa uku dake kan hanyar

Titin Abuja-Kaduna: El-Rufa'i ya bada shawarar tayar da wasu garuruwa uku dake kan hanyar

  • Gwamnatin jihar Kaduna na shawara kan yadda za'a dawo da zaman lafiya da samar tsaro a jihar
  • Titin Kaduna zuwa Abuja ya zama hanya da yafi kowani hanya a Najeriya hadari sakamakon hare-haren yan bindiga
  • Malam Nasir El-Rufa'i ya bada shawaran tayar da wasu garuruwa uku dake kan titin

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna,Nasir El-Rufai, a ranar Alhamis ya bada shawaran tayar da kauyukan Katari, Rijana da Akilibu, dake kan titin babbar hanyar Kaduna-Abuja.

Yace masu kaiwa yan bindiga bayanai ne suka cika wadannan kauyuka.

El-Rufa'i ya bayyana hakan ne yayin karban rahoton irin hare-haren yan bindigan da jihar Kaduna ta fuskanta tsakanin watar Junairu da Maris, rahoton TheNation.

Ya ce yanzu yan ta'adda sun tashi daga Arewa maso gabas, sun shiga Arewa maso yamma.

Kara karanta wannan

Cikin katatafaren kadarorin da suka tsunduma AGF Ahmed Idris a komar EFCC

A cewarsa, idan ba'a dau mataki da wuri ba abinda ke zai faru a yankin Arewa maso yamma sai ya fi Arewa maso gabas muni.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

El-Rufa'i
Titin Abuja-Kaduna: El-Rufa'i ya bada shawarar tayar da wasu garuruwa uku dake kan hanyar Hoto: Governor of Kaduna
Asali: Twitter

Gwamnan yace:

"Wannan rahoto ya tada mana hankali. Abin damuwa na farko shine bayyanan yan Boko Haram da Ansaru a Birnin Gwari da Chikun."
"Daga cikin wadanda aka sace a jirgin kasa tsohon aboki na ne wanda aka sake bayan biyan kudin fansa."
"A lokacin da yake hannunsu, yan bindigan na fadin cewa dazukan Kaduna sun fi na Sambisa dadi, saboda haka kawai su dawo nan."
"Abu na hudu shine rawar da Rijana, Katari da Akilibu ke takawa a wannan hare-hare, na rashin tsaron Titin Kaduna-Abuja."
"Muna shawarar yadda zamu yi da wadannan kauyuka, ko a mayar da su Kagarko, ku kuma mu tayar da su gaba daya."

Kara karanta wannan

Boka ya dirkawa matar aure ciki, rikici ya barke tsakaninsa da mijinta: Ga labarin dalla-dalla

Adadin mutanen da ake kashe da wadanda akayi garkuwa dasu a Kaduna cikin watanni 3

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i ya bayyana damuwarsa bisa yawaitan yan ta'adan Ansaru da na Boko Haram a jihar Kaduna.

Gwamnan ya bayyana cewa hakazalika akwai sabon alaka dake gudana yanzu tsakanin yan bindiga masu garkuwa da mutane da yan Boko Haram.

A cewarsa, wannan alaka ta haifar da harin da aka kai jirgin kasan Abuja-Kaduna ranar 28 ga Maris, 2022.

Ya bayyana haka ne a zaman majalisar tsaron jihar na watanni uku-uku da kwamishanan tsaron jihar, Samuel Aruwan, ke gabatar da bayanan tsaro, rahoton TVCng

Malam El-Rufa'i a jawabinsa ya kara da cewa yanzu yan ta'adda sun fara dasa bama-bamai a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng