Sun daina ta'addanci: Akwai akalla tubabbun 'yan Boko Haram 53,262 a hannun sojoji, DHQ

Sun daina ta'addanci: Akwai akalla tubabbun 'yan Boko Haram 53,262 a hannun sojoji, DHQ

  • Rahoton rundunar sojin Najeriya ya bayyana yadda 'yan ta'addan Boko Haram ke ci gaba da mika wuya ga gwamnati
  • Rahoton ya ce ya zuwa yanzu akwai tubabbun 'yan ta'adda sama da 50,000 da ke hannun gwamnatin bayan tubarsu
  • Hakazalika, rundunar ta bayyana kuma adadin ayyukan da sojoji suka yi a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya

Abuja - Hedikwatar tsaro ta najeriya a jiya ta ce ‘yan ta’addan Boko Haram 53,262 ne suka mika wuya ya zuwa ranar 16 ga watan Mayu, rahoton Daily Trust.

Hedkwatar ta ce akalla ‘yan Boko Haram 1,627 ne da iyalansu, wadanda suka hada da maza 331, mata 441 da kananan yara 855, sun mika wuya ga sojojin a wurare daban-daban tsakanin 1 ga Mayu zuwa 14 ga Mayu.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Hatsarin mota ya rutsa da dan takarar gwamnan APC a Abuja

Darakta, Ayyukan Yada Labarai na Tsaro, Maj.-Gen. Bernard Onyeuko, ya bayyana haka ne a Abuja a wani taron manema labarai kan ayyukan sojojin tsakanin 28 ga Afrilu zuwa 19 ga Mayu.

Yan Boko Haram sama da 50,000 sun mika wuya
Mun bar ta'addanci: 'Yan Boko Haram 53,262 ne suka mika wuya ga sojoji, DHQ | Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

The Nation ta rahoto shi yana cewa:

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

“Tsakanin 1 – 14 ga Mayu 2022, jimillar ‘yan ta’addar Boko Haram 1,627 da iyalansu sun mika wuya ga sojoji a wurare daban-daban."

Ya ce dakarun Operation Hadin Kai sun kashe ‘yan ta’adda 43, sun kama 20 tare da kubutar da mutane 63 da aka sace duk a yankin Arewa maso Gabas cikin makwanni uku.

Ya ce sojojin sun kashe wani kwamandan Boko Haram Abubakar Sarki a dajin Sambisa da ke Yuwe a karamar hukumar Konduga a jihar Borno, kamar yadda rahotannin baya suka tabbatar.

Ya ce sojojin, a wani samame na hadin gwiwa da sojojin kasa da na sama suka yi a lokacin da suke gudanar da aikin share fage, sun kuma kashe babban hakimin yankin Gaita na Boko Haram, Malam Shehu da wasu daga cikin sojojin sa.

Kara karanta wannan

Nasara daga Allah: Sojoji sun kashe wani kasurgumin kwamandan Boko Haram

Ya ce sojojin sun kuma kama Mallam Modu Goni, wani dan ta’adda da ke sayar da kayayyaki a Kasuwar Bunin Yadi ga 'yan ta'adda bisa wani rahoto na hankali.

An rahoto shi yana cewa:

“A ci gaba da gudanar da ayyukanta, a ranar 17 ga Mayu, 2022, an kama Mallam Modu Pantami a wajen kauyen Benished a karamar hukumar Kaga a lokacin da yake kokarin jigilar kayayyaki masu yawa da ya saya domin kaiwa ga ‘yan ta’adda a Gomari kauyen dake karamar hukumar Fere a jihar Borno.
"Sojoji sun gudanar da wani harin kwantan bauna a magamar 'yan ta'adda a kauyen Kaidieri, a sanadin harin aka kashe 'yan ta'adda biyar tare da kwato makamai iri-iri da alburusai daban-daban daga hannun 'yan ta'addan."

Shekara da mutuwar Shekau: Waiwaye ga hare-haren Boko Haram 12 da suka girgiza duniya

A wani labarin, a yau ne shugaban 'yan ta'addan Boko Haram Abubakar Shekau ke cika shekara guda da barin duniya, tun bayan da rahotanni suka ce ya sheke kansa a wani artabu da 'yan uwansa 'yan ta'adda da ake kyautata zaton 'yan ISWAP ne.

Kara karanta wannan

Shekara da mutuwar Shekau: Waiwaye ga hare-haren Boko Haram 12 da suka girgiza duniya

Boko Haram dai kungiya ce ta ta'addanci da ta shahara a Najeriya da kasashen nahiyar Afrika makwabta, inda ta yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama da kuma salwantar dukiyoyi da ababen more rayuwa.

An san kungiyar da kai hare-hare kan ababen gwamnati, daidaikun jama'a har ma da wuraren ibada da makarantu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel