Kundumbala: Farfesan da aka garkame ya yi ‘yunkurin’ bada cin hancin N16m ya na tsare

Kundumbala: Farfesan da aka garkame ya yi ‘yunkurin’ bada cin hancin N16m ya na tsare

  • Independent Corrupt Practices and Other Related Offences Commission ta na karar John Kester Ifeanyichukwu
  • Hukumar ta fadawa kotu cewa Farfesa John Kester Ifeanyichukwu ya nemi ba jami’inta cin hancin Dala $50, 000
  • Farfesan ya yi alkawarin zai biya ma’aikacin wadannan kudi saboda a kawo cikas wajen bincikensa da ake yi

Abuja - Hukumar nan ta ICPC ta gurfanar da wani mai suna John Kester Ifeanyichukwu a gaban babban kotun tarayya a bisa zargin laifin bada cin hanci.

The Cable ta ce hukumar ICPC ta na tuhumar John Kester Ifeanyichukwu wanda Farfesa ne a kan yunkurin ba wani ma’aikacinta cin hancin Dala $40, 000.

Kamar yadda darajar Dala ta ke a kasuwar canji a yau, wannan kudi ya haura Naira miliyan 16.

Kara karanta wannan

Takarar Amaechi ta na ta karfi, Buratai da tsohon IGP su na mara masa baya a zaben 2023

Wani jawabi da ya fito daga bakin mai magana da yawun ICPC, Azuka Ogugwa a Facebook ya bayyana cewa an kai karar wajen Alkali AO Otaluka a Abuja.

Laifin da ake zargin Farfesan ya aikata shi ne yi wa jami’in hukumar alkawarin fam Dala 50, 000 da gida a Abuja domin ya lalata bincike da ake yi a kansa.

Rahoton ya ce Ifeanyichukwu ya nemi ma’aikacin na ICPC ya karbo masa na’urorinsa da ke hannun hukumar, wadanda ake amfani da su wajen bincike.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

ICPC Abuja
Hedikwatar hukumar ICPC Hoto: icpc.gov.ng
Asali: UGC

Na’urorin sun hada da komfutoci biyu; MacBook S/N CIML8BUGDTY3 da MacBook S/N W80204J7ATN da kuma wayar salula kirar IPhone 11 Pro.

Jawabin kakakin ICPC

“Fadar shugaban kasa ta kawo karar John Kester Ifeanyichukwu a bisa zargin laifuffukan da suka shafi rashin gaskiyam, kwace da kuma satar kudi.
ICPC a kara mai lamba: CR/025/2022, ta sanar da kotu yadda wanda ake zagi ya nemi jami’inta ya sato wayarsa ta IPhone da kuma komfutarsa.

Kara karanta wannan

Jam’iyyar NNPP ta fitar da duk wadanda za su yi mata takaran zaben 2023 a jihar Kano

Za ayi haka da nufin maye gurbinsa da na’urorin karya da hadiminsa zai kawo a madadinsu.”

- Azuka Ogugwa

Alkali ya daga shari'a

Kamar yadda PM News ta kawo rahoto a ranar Talata, hukumar ta na zargin vewa wannan danyan aiki ya sabawa sashe na 18 (b) na dokar ICPC ta 2000.

Mai shari’a ya bada belin Farfesa Ifeanyichukwu a kan N10m bayan ya amsa cewa bai da laifi. Za a cigaba da sauraron karar ne a ranar 21 ga watan Yunin 2022.

Fayemi v Oshiomhole

A makon nan labari ya zo cewa Adams Oshiomhole ya ce Gwamnan jihar Ekiti Kayode Fayemi ya taba nemansa ya murde wani zabe a lokacin yana rike da APC.

Kayode Fayemi ya karyata wannan zargi, ya ce bai taba tunkarar Oshiomhole da maganar magudi ba. Fayemi ya zargi Oshiomhole da karfa-karfa wajen jagoranci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel