Magu ya yi ritaya kafin aka amince da yi masa karin girma – Ministan harkokin yan sanda

Magu ya yi ritaya kafin aka amince da yi masa karin girma – Ministan harkokin yan sanda

  • Ministan harkokin yan sanda, Maigari Dingyadi, ya tabbatar da cewa tsohon mukadasshin shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu, ya yi ritaya kafin aka yi masa karin girma
  • Dingyadi ya kuma bayyana cewa hukumar PSC da ke karkashin fadar shugaban kasa ce ke da amsa kan dalilin yi masa karin girman
  • Sai dai kuma ya bayyana cewa ritayarsa ba zai hana shi fuskantar duk wasu matakan ladabtarwa ba idan bukatar hakan ya taso

Abuja - Karin girman da aka yiwa tsohon shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC), Ibrahim Magu, zuwa matsayin mataimakin sufeto janar na yan sanda (AIG), a kwanan nan ya zo ne bayan ya yi ritaya.

Ministan harkokin yan sanda, Maigari Dingyadi, ne ya bayyana hakan a yayin da ya bayyana a matsayin bako a taron tattaunawa na mako da tawagar shugaban kasa kan sadarwa ta yi a fadar shugaban kasa, Abuja, The Nation ta rahoto.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa ya rigamu gidan gaskiya

Magu ya yi ritaya kafin a amince da yi masa karin girma – Ministan harkokin yan sanda
Magu ya yi ritaya kafin a amince da yi masa karin girma – Ministan harkokin yan sanda Hoto: The Nation
Asali: Facebook

A ranar Litinin ne hukumar yan sanda ta PSC ta amince da karin girma ga tsohon shugaban na EFCC a daidai lokacin da ritayarsa daga rundunar yan sanda ya kai, kasancewar ya cika shekaru 60 a ranar 5 ga watan Mayun 2022.

Kwamitin shugaban kasa karkashin jagorancin Justis Ayo Salami na ta binciken Magu, inda tuni ya gabatar da rahotonsa wanda ya bayar da shawarar yiwa Magu ritaya a 2020.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Da aka tambaye shi kan dalilin da yasa aka yi masa karin girma, ministan ya ce hakkin hukumar PSC wacce ke karkashin fadar shugaban kasa ne samar da amsar.

Amma ya bayar da tabbacin cewa an rigada an yiwa Magu ritaya, yana mai cewa ritayarsa ba zai hana shi fuskantar duk wasu matakan ladabtarwa ba idan bukatar hakan ya taso, rahoton Daily Post.

Kara karanta wannan

Sokoto: Bishop Kukah ya yi martani kan kashe dalibar da ta yi batanci ga Annabi

Daga karshe: Duk da kama Magu da aikata rashawa, gwamnati ta kara masa matsayi

A baya mun kawo cewa hukumar aikin ‘yan sanda ta tabbatar da karin girma ga tsohon shugaban riko na hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC), Mustafa Ibrahim Magu zuwa mataimakin sufeto janar na ‘yan sanda, tare da wasu mutane biyar.

AIG Magu Ibrahim wanda ke gargarar yin ritaya, shi ne wanda ya fi kowa girma a tsararrakinsa kuma ya kasa samun karin girma har sau biyu bayan da ya dawo hukumar ‘yan sanda daga EFCC, Channels Tv ta ruwaito.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da hukumar ta tabbatar da karin girma ga John Ogbonnaya Amadi a matsayin mataimakin Sufeto Janar na ‘yan sanda, domin maye gurbin marigayi DIG Joseph Egbunike wanda ya wakilci Kudu Maso Gabas a tawagar ‘yan sanda.

Asali: Legit.ng

Online view pixel