El-Rufai: Ƴan Boko Haram Da ISWAP Sun Yada Zango a Ƙananan Hukumomi 2 a Kaduna

El-Rufai: Ƴan Boko Haram Da ISWAP Sun Yada Zango a Ƙananan Hukumomi 2 a Kaduna

  • Gwamnatin Jihar Kaduna ta bayyana batun hare-hare da ta’addancin da kungiyoyin Boko Haram da ISWAP su ke yi a jihar, inda su ke cin karensu babu babbaka
  • Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar, Samuel Aruwan ya bayyana hakan yayin da ya ke gabatar da rahoton watanni 4 na farkon shekarar 2022
  • A cewarsa, tuni mambobin kungiyoyin su ka mamaye wasu bangarori na Birnin Gwari da karamar hukumar Giwa inda su ke ta jan ra’ayin ‘yan kauye da kyautuka

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kaduna - Gwamnatin Jihar Kaduna ta bayyana damuwarta akan yadda kungiyoyin ta’addanci su ke ta aiwatar da harkokinsu a cikin jihar, Channels TV ta ruwaito.

Yayin gabatar da rahotannin watanni hudu na farkon shekarar 2022 ga majalisar tsaron jihar, Kwamishinan harkokin cikin gida da tsaro, Samuel Aruwan ya ce yan kungiyar Ansaru da Boko Haram sun baje kolin ta’addancinsu a Birnin Gwari da karamar hukumar Giwa.

Kara karanta wannan

Zagin Annabi: Kungiyoyin CAN da JNI sun gargadi matasa a kan yin kalaman tunzura

El-Rufai: 'Yan Boko Haram Da ISWAP Sun Shigo Jihar Kaduna
'Yan Boko Haram Da ISWAP Sun Shigo Jihar Kaduna, El-Rufai Ya Nuna Damuwarsa. Hoto: Daily Trust.
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

‘Yan ta’addan sun fara jan ra’ayin mazauna kauyaku

Aruwan ya ce wasu ‘yan ta’adda sun fara jan ra’ayin mazauna kauyaku da kyautuka yayin da su ke horar da su akan ta’addanci.

Gwamna El-Rufai ya nuna damuwarsa kamar yadda Vanguard ta nuna, akan yadda ‘yan ta’addan su ke matsowa daga yankin Arewa maso Gabas zuwa Arewa maso Yamma don ci gaba da baje kolin ta’addanci.

Ya kara da cewa wadanda su ka kai harin jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna ma ‘yan ta’addan Boko Haram ne.

Gwamnan ya kara da bayyana damuwarsa karara akan yiwuwar gudanar da zaben 2023 a Jihar Kaduna in har ba a kawo garanbawul ga matsalar tsaro ba.

Cikin watanni hudu, mutane 360 ne su ka rasa rayukansu

Sai dai Aruwan ya ce wadanda ake zargin ‘yan ta’adda ne sun halaka fiye da mutanen 360 daga watan Janairu zuwa Afirilu.

Kara karanta wannan

Atiku: Da Zarar Na Zama Shugaban Ƙasa Ƴan Bindiga Za Su 'Shiga Uku'

Mazabar Kaduna ta tsakiya ta fi ko wanne yanki fuskantar ta’addanci inda mutane 214 su ka rasa rayukansu kamar yadda kwamishinan ya bayyana.

Aruwan ya kula da cewa ‘yan bindiga sun yi garkuwa da mutane 1,389 daga wurare daban-daban na Jihar Kaduna a cikin watanni hudun, ciki har da mutane 62 da aka sace a harin ranar 28 ga watan Maris wanda aka kai wa jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna.

'Yan Ta'addan Da Suka Kai Hari Sansanin Sojoji Na Kaduna Sun Ɗanɗana Kuɗarsu, Lai Mohammed

A bangare gudan, Gwamnatin Tarayya, a ranar Laraba ta ce yan ta'addan da suka kai hari sansanin sojoji da ke Birnin Gwari a Kaduna sun sha azaba a hannun sojoji a yayin da suka fatattake su, rahoton Daily Trust.

Ministan Labarai da Al'adu, Alhaji Lai Mohammed, ne ya bayyana hakan yayin da ya ke amsa tambayoyi kan tsaro bayan taron FEC da Shugaba Muhammadu Buhari ya jagoranta a Aso Villa a Abuja.

Kara karanta wannan

Batanci: Ku girmama addinin mutane da abinda suka yi imani da shi sai a zauna lafiya, El-Rufa'i

Rahotanni sun bayyana cewa sojoji 11 ne suka riga mu gidan gaskiya yayin da wasu da dama suka jikkata yayin harin na ranar Talata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164