Karin bayani: APC ta bayyana sabbin ranakun zaben fidda gwani na shugaban kasa da sauran kujerun siyasa

Karin bayani: APC ta bayyana sabbin ranakun zaben fidda gwani na shugaban kasa da sauran kujerun siyasa

  • Jam'iyya mai mulki ta APC ta sanar da sabbin ranakun zabukan fitar da gwani na masu takarar shugaban kasa da sauran kujerun siyasa na kasar nan
  • Sakataren yada labarai na jam'iyyar, Felix Morka, ya sanar da cewa kwamitin ayyuka na kasa na jam'iyyar ya aminta da sabbin ranakun
  • An fitar da ranar 29 ga watan Mayun 2022 a matsayin ranar da za a yi zaben fitar da gwani na 'yan takarar shugabancin kasa

Abuja - Jam'iyyar All Progressive Congress mai mulki ta saka sabbin ranakun zabukan fidda gwani na shugaban kasa da sauran kujerun siyasa.

Wannan na kunshe ne a wata takarda da sakataren yada labarai na jam'iyyar, Felix Morka ya saki, jaridar Punch ta bayyana rahoton.

Kara karanta wannan

Gwamnan 2023: Yadda masoya APC a Sokoto ke neman ayi zaben fidda gwani na kato bayan kato

Kwamitin ayyuka na kasa na jam'iyyar ya amince da sabbin ranakun a taron da ya yi a ranar Laraba.

Morka ya ce za a yi zaben fitar da gwani na shugabancin kasas ana jam'iyyar a ranar 29 ga watan Mayun 2022.

Da duminsa: APC ta bayyana sabbin ranakun zaben fidda gwani na shugaban kasa da sauran kujerun siyasa
Da duminsa: APC ta bayyana sabbin ranakun zaben fidda gwani na shugaban kasa da sauran kujerun siyasa. Hotto daga punchng.com
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Jam'iyyar mai mulki tun farko ta saka ranar 30 ga watan Mayu da ranar 1 ga watan Yuni domin yin zaben fidda gwaninin.

Morka ya ce an saka ranar 26 ga watan Mayu domin zaben fidda gwani na 'yan takarar kujerar gwamnoni da 'yan majalisar wakilai, lamarin da a baya aka saka ranakun 20 ga watan Mayu da 24 ga Mayu domin yin su.

Hakazalika, za a yi zaben fidda gwani na majalisar tarayya da majalisun jihohi a ranar 27 ga watan Mayu a maimakon 25 da 22 ga watan Mayun da aka saka tun farko.

Kara karanta wannan

2023: Ƴan Takara 3,000 Ne Za Su Fafata Don Neman Tikitin Takarar Majalisun Jihohi a APC

Morka ya kara da cewa, za a saurari daukaka kara kan zaben fidda gwanin na gwamnoni da 'yan majalisar wakilai a ranar 27 ga watan Mayu yayin da za a saurari na majalisar dattawa da majalisar jiha a ranar 30 ga watana Mayu.

A dayan bangaren, za a yi zaben fitar da gwani na jam'iyyar adawa ta PDP tsakanin ranakun 28 ga Mayu zuwa 29.

The Cable ta ruwaito cewa, a yayin da jam'iyya mai mulki za ta yi amfani da filin wasa na Eagle Square, jam'iyyar adawa ta PDP za ta yi amfani da filin wasa na MKO Abiola duk a Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel