Ba Zan Bari Maƙiyan El-Rufai Su Kawo Mana Cikas a Hajjin 2022 Ba, Shugaban Hukumar Jin Dadin Alhazai

Ba Zan Bari Maƙiyan El-Rufai Su Kawo Mana Cikas a Hajjin 2022 Ba, Shugaban Hukumar Jin Dadin Alhazai

  • Dr Yusuf Yakubu Alrigasiyu, babban sakatare a hukumar kula da ji dadin maniyyata na jihar Kaduna ya shiga ofishinsa a hedkwatar hukumar a Kaduna
  • Alrigasiyu ya ce akwai wasu makiyan Gwamna Nasir El-Rufai da ke neman ganin an samu matsala yayin aikin hajjin amma ba zai bari hakan ta faru ba
  • Dr Alrigasiyu ya nemi hadin kan dukkan ma'aikatan hukumar yana mai cewa zai musu adalci amma ya bukaci kuma su kasance masu aiki tukuru don ganin anyi nasara

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Kaduna - Babban Sakataren Hukumar Jin Dadin Maniyyata na Jihar Kaduna, Dr Yusuf Yakubu Alrigasiyu, ya sha alwashin ba zai bari yan siyasa da ke gaba da gwamna Nasir El-Rufai, su kawo cikas ga ayyukan Hajji na 2022 a jihar ba.

Kasancewarsa wakilin gwamna a hukumar, Alrigasiyu ya ce zai yi duk mai yiwuwa don tabbatar da ganin an yi aikin hajjin cikin nasara.

Kara karanta wannan

Da zafi-zafi: Hotunan Osinbajo yayin da ya ziyarci wajen da tukunyar gas ta fashe a Kano

Ba Zan Bari Maƙiyan El-Rufai Su Kawo Mana Cikas a Hajjin 2022 Ba, Shugaban Hukumar Jin Dadin Alhazai
Ba Zan Bari Maƙiyan El-Rufai Su Kawo Mana Cikas a Hajjin 2022 Ba, Alrigasiyu. Hoto: Daily Trust.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Da ya ke jawabi jim kadan bayan shiga ofishinsa a hedkwatar hukumar da ke jihar, Alrigasiyu ya yi ikirarin cewa akwai wasu yan adawa na siyasa da za su fake da duk wani karamin kuskure don sukar gwamnan da shugabannin hukumar, rahton Daily Trust.

"Na zo nan ne a matsayin wakilin gwamna don haka ba zan bari yan adawa na siyasa na ciki da waje su kawo cikas ga aikinmu ba.
"Irin wadannan mutanen suna jira su ga mun yi kuskure don su soki gwamnan mu ko mu. Ba zan bari hakan ta faru ba," in ji shi.

Ya nemi hadin kai da goyon bayan ma'aikatan hukumar domin ya samu nasara a yayin aikinsa, yana mai alkawarin yi wa kowa adalci.

Yayin da ya ce ya yi imani da aiki tukuru, ya yi kira ga ma'aikatan su mayar da hankali su jajirce wurin aikinsu.

Kara karanta wannan

2023: Igbo Ba Abin Yarda Bane, Ba Mu Amince Su Mulki Ƙasa Ba, Ƙungiyoyin Arewa

Shugaban riko na hukumar, Hajiya Hannatu Zailani, ta bashi tabbacin goyon bayan ma'aikatan hukumar don ganin an samu nasarar aikin hajjin na 2022.

Kaduna 2023: Za Mu Amince Da Kama Karya Ba, Ɗan Takarar Gwamna, Sha'aban Ya Yi Watsi Zaɓin El-Rufa'i

A wani rahoto, Alhaji Sani Sha’aban, wani dan takarar gwamna a Jihar Kaduna karkashin jam’iyyar APC ya nuna rashin amincewarsa da dan takarar gwamnan da Nasir El-Rufai, gwamnan Jihar Kaduna ya mara wa baya a zaben 2023 da ke karatowa, rahoton Daily Trust.

Sha’aban ya bayyana hakan ne yayin da manema labarai su ke tattaunawa da shi a gidansa cikin kwananin karshen mako, Nigerian Tribune ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164