Innalillahi: Mummunan Hatsarin Mota Ya Kashe Mutum 20 a Hanyar Kaduna Zuwa Abuja

Innalillahi: Mummunan Hatsarin Mota Ya Kashe Mutum 20 a Hanyar Kaduna Zuwa Abuja

  • Mutane 20 sun riga mu gidan gaskiya sakamakon hatsarin mota da ya afka da su a hanyar Kaduna zuwa Abuja
  • Rahotanni sun nuna cewa motar bas da ke dauke da mutum 22 ne ya daki wata tirela da ke ajiye a gefen hanya ya shiga karkashinta ya kama da wuta
  • Hukumar Kiyayye Hadura FRSC ta tabbatar da afkuwar hatsarin inda ta ce tana zargin gyangyadi da direban bas din ke yi ne ya janyo hatsarin

Mutane 20 ne aka tabbatar sun riga mu gidan gaskiya sakamakon wani mummunan hatsarin mota da ya faru tsakanin motar bas da tirela a babban hanyar Kaduna zuwa Abuja, The Punch ta rahoto.

Daily Trust ta rahoto cewa cikin wadanda hatsarin ya ritsa da su, 17 maza ne, biyu mata ne sannan akwai karamin yaro daya, yayin da mutum biyu sun tsira.

Kara karanta wannan

Hanyar Abuja-Kaduna: A jiya Talata kadai, mutum 20 sun kone kurmus a hadarin mota, yan bindiga sun sace 30

Innalillahi: Mummunan Hatsarin Mota Ya Kashe Mutum 20 a Hanyar Kaduna Zuwa Abuja
Hatsarin Mota Ya Kashe Mutum 20 a Hanyar Kaduna Zuwa Abuja. Hoto: The Nation.
Asali: Facebook

Motar bas din ta daki tirelar ne da aka ajiye ta a gefen titi misalin karfe 5.00 na asubahi kamar yadda rahoto ya tabbatar.

Hukumar FRSC ta tabbatar da afkuwar hadarin

Hafiz Muhammad, shugaban Hukumar Kiyayye Hadura ta Kasa, FRSC, reshen Jihar Kaduna ya tabbatar da afkuwar hatsarin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, suna zargin cewa gyangyadi da direban bas din ke yi ne saboda tafiyar dare ta saka shi ya daki tirelar.

"Bas din ta fada karkashin tirelar siminti ta kamfanin BUA, sai ta kama da wuta. Mutum 22 ke cikinta, inda 20 cikinsu suka rasu.
"An ce tirelar ajiye ta ke a lokacin da bas din ta dake ta, ta kuma shiga karkashinta. Abin tsoro ne matuka kasancewar mun dade muna gargadin direbobi game da tafiyar dare," a cewar Hafiz.

Shugaban na FRSC ya ce babu wata doka da ta hana tukin dare kai tsaye, amma akwai matukar matsala tattare da hakan don mafi yawancin haddura da ake yi a hanyar cikin dare suka faruwa.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Yan bindiga sun sake kai kazamin hari kan matafiya a hanyar Abuja-Kaduna

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164