Damfarar N80bn: ASUU ta zunɗi AGF, ta ce FG ta yi watsi da tsarin IPPIS
- Kungiyar malamai masu koyarwa na jama'a tayi kira ga gwamnatin tarayyar da tayi fatali da tsarin biyan ma'aikata na IPPIS da ta dauka tsawon lokaci tana biyan ma'aikata albashi
- ASUU ta fadi hakan ne yayin martani game da cafke akawu janar na tarayya da EFCC tayi bayan an zarge shi da almundahanar kudi har N80 biliyan
- Kungiyar ta bukaci EFCC da ta tabbatar ta tsananta bincike tare da gurfanar da Idris gaban kotun, sannan ta bayyana yadda tsarin IPPIS ke cure almundahana wuri guda
A ranar Talata, kungiyar malaman jami'a masu koyarwa (ASUU) ta bukaci gwamnatin tarayya da tayi watsi da tsarin biyan ma'aikata na IPPIS da take amfani dashi wajen biyan ma'aikatan tarayya albashi.
ASUU ta yi martani game da cafke akawu janar na tarayya, Ahmad Idris da hukumar EFCC tayi bisa zarginsa da almundahana, tare da sunkuce N80 biliyan jaridar Newswire ta ruwaito.
Daily Trust ta rahoto cewa, kungiyar ta bukaci EFCC da ta tsananta bincike gami da gurfanar da Idris kotu don tabbatar an kawo karshen lamarinsa.
Shugaban ASUU, farfesa Emmanuel Osodeke, a wata tattaunawa da Daily Trust a jiya, ya ja kunne kan kada a yi rufa-rufa a lamarin, inda ya ce "mutanen banza sun cancanci horo duba da manufar wannan mulkin."
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A cewarsa: "Mun fadi kuma muna cigaba da fada tsarin biyan ma'aikata na IPPIS damfarace. Haka zalika, mun ce akawu janar na tarayya 'dan damfara ne, kawai suna amfani da IPPIS ne don cure sabgogin damfara wuri daya, wanda shi ne ofishin akawu janar, kuma mun gane hakan. Wannan shine matsayarmu.
"Wannan tsarin IPPIS din, zan iya fada muku a halin yanzu da nake magana, cewa ba a biya da yawan ma'akatanmu albashin watanni 13, watanni takwas, da watanni tara ba, amma suna fada wa gwamnati cewa suna amfani da shi ne don dakatar da almundahana."
Hanyar Abuja-Kaduna: A jiya Talata kadai, mutum 20 sun kone kurmus a hadarin mota, yan bindiga sun sace 30
Sai dai kuma, hukumar watsa labarai, tsari da tabbatar da gaskiya (CMPA) a ranar Talata tayi kira ga gaggauta gurfanar da Idris.
A wata takarda da CMPA ta saki ta hannun daraktan sadarwanta, Ibrahim Uba Yusuf, ta ce: "yana da mahimmaci a san cewa kama AGF ya zo ne bayan korafi daban-daban da a ka yi tayi akan ofishin, wanda ke lura da tsarin biyan ma'aikata na IPPIS ba kawai curewa ya yi ba, sai dai ma da ya bunkasa almundahana."
Yajin ASUU: Tashin hankali yayin da sojoji ke harba bindigogi a wurin zanga-zangar dalibai
A wani labari na daban, ana zargin cewa wasu jami’an sojin Najeriya sun kai farmaki wurin da dalibai ke gudanar da zanga-zanga a garin Akure na jihar Ondo a ranar Talata.
Daliban sun fita zanga-zangar kwana biyu a jihar ne saboda yajin aikin da kungiyar malaman jami’o’i ASUU ta shiga. Bidiyon da Punch tace ta samo ya nuna yadda tarin sojoji ke tafiya dauke da bindigogi, tare da mota da ke bin su a baya.
An ji karar harbe-harbe a lokacin da suke tafiya yayin da wasu daga cikin daliban suka ruga da gudu cikin firgici.
Asali: Legit.ng