Batanci: Ku girmama addinin mutane da abinda suka yi imani da shi sai a zauna lafiya, El-Rufa'i

Batanci: Ku girmama addinin mutane da abinda suka yi imani da shi sai a zauna lafiya, El-Rufa'i

  • Gwamna Malam Nasiru El-Rufa'i na jihar Kaduna ya gargaɗi mutane su rinka girmama Addinan sauran mutanen da suke zaune da su
  • Gwamnan ya yi wannan magana ne bayan taron duba halin tsaron kasar nan biyo bayan abinda ya faru a Sokoto
  • Ya ce gwamnatinsa da hukumomin tsaro za su cigaba da bibiyar lamarin sau da ƙafa da kokarin dakile ta da zaune tsaye

Kaduna - Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa'i, ya roki mazauna jiharsa su girmana Addinai da Al'adun abokan zaman su kuma su nisanci cin mutunci ta kowace hanya.

Gwamnan ya yi wannan rokon ne a wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan, ranar Talata.

Daily Trust ta rahoto wannan sanarwan ta zo ne bayan sake duba halin da tsaron ƙasar nan ke ciki biyo bayan abinda ya faru a Sakkwato na yin batanci ga Annabi SAW.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Yan bindiga sun sake kai kazamin hari kan matafiya a hanyar Abuja-Kaduna

Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai.
Batanci: Ku girmama addinin mutane da abinda suka yi imani da shi sai a zauna lafiya, El-Rufa'i Hoto: Nasir El-Rufai/faceboon
Asali: Facebook

Gwamna ya yaba wa shugabannin Addinai, Sarakuna da shugabannin al'umma da sauran hukumomin tsaro bisa namijin kokarinsu wajen tabbatar da zaman lafiya a Kaduna.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

A sanarwan da Aruwan ya fitar, ya ce:

"Gwamnati na kira ga iyaye su wa'azantar da 'ya'yansu da mutanen gundumarsu kan aikata kyawawan ayyuka kuma su guji duk wani abu da bara gurbi ka iya shiga ciki su ta da yamutsi."
"Haka nan gwamnati ta na kira da mutane, domin dorewar tsaro da zaman lafiya, su girmama Addinin da sauran mutane abokan zaman suka yi imani da shi da al'adun su, su nesanci batanci kowane iri."
"Daɗin daɗawa gwamnatin ta ƙara jaddada cewa ba zata lamurci komai ba sai biyayya da bin doka kuma ba zata taɓa amince wa da ɗaukar doka a hannu ba."

Zamu cigaba da bibiyar halin da ake ciki - El-Rufai

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Yan bindiga sun aike da sakon sunayen kananan hukumomi 9 da zasu kai hari

Gwamnan ya ce gwamnatinsa da hukumomin tsaro zasu cigaba da sa ido da bibiyar lamarin sau da ƙafa, kuma zasu yi aiki tukuru domin dakile duk wani abu da ka iya saɓa wa doka.

A wani labarin kuma Wani ɗalibin kwalejin fasaha ya mutu yana tsaka da saduwa da budurwarsa a Hotel

Wani ɗalibi da ya gama Diploma a matsayin mafi hazaƙa, Daniel, ya mutu ya na tsaka da holewa da budurwarsa a Otal.

Hukumar makarantar Ibadan Poly inda ya ke karatun babban Diploma ta ce lamarin babu daɗi, zata cigaba da shawartar dalibai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262