Muddin ba'a yi sulhu da ASUU ba, ba zamu bari ayi zabe ba: Daliban Jami'a

Muddin ba'a yi sulhu da ASUU ba, ba zamu bari ayi zabe ba: Daliban Jami'a

  • Dalibai jami'a sun lashi takobin cewa ba zasu bari ayi zabe ba muddin ASUU bata yanje daga yajin aiki ba
  • Tun watan Febrairun shekarar nan, kungiyar malaman jami'o'in Najeriya ASUU sun shiga yajin aiki
  • Makon nan za'a fara gudanar da zabukan fidda gwanin jam'iyyun siyasa don zaben 2023

Osun - Daliban jami'ar Obafemi Awolowo University (OAU), Ile-Ife, jihar Osun sun cigaba da zanga-zanga bisa yajin aikin ASUU dake gudana.

Daliban sun lashi takobin cewa ba zasu bari ayi zabe ba muddin ba'a bude musu makarantu sun koma aji ba, rahoton Vanguard.

Daliban sun taru gaban kofar makarantar misalin karfe 7 na safe da littafan rubutu inda sukayi ikirarin ko anan Malamansu su zo suyi musu karatu.

Hakazalika suka tare babban titin Ife-Ibadan misalin karfe 10 na safe wanda hakan yayi sanadiyar cinkoson motoci.

Kara karanta wannan

Gwamnonin APC sun sa labule bayan Buhari ya faɗa musu matsayarsa kan wanda zai gaje shi a 2023

Muddin ba'a yi sulhu da ASUU, ba zamu bari ayi zabe ba: Daliban Jami'a
Muddin ba'a yi sulhu da ASUU, ba zamu bari ayi zabe ba: Daliban Jami'a
Asali: Depositphotos

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Mataimakiyar shugabar daliban jami'ar, Aworanti Grace, ta bayyana cewa ai tuni sun gargadi gwamnati cewa ta biya bukatun ASUU ko kuwa ba zasu bari zabe ya yiwu ba.

Tace:

"Mun gargadi gwamnati cewa kada ta bari dalibai su fara zanga-zanga kafi suyi sulhu da ASUU. Gashi lokaci ya kawo mu, ba zamu daina zanga-zanga ba sai an bude makarantu."
"Ba zamu bari ayi wani zabe ba, musamman zaben gwamna a Osun da za'a yi a watan Yuli da kuma zaben kasa da za'ayi a 2023."

Legit Hausa ta tuntubi wansu dalibi mai karatu a jami'a kan halin da dalibai suka shiga kan wanna yajin aikin.

Sule Ya'u, dan aji biyu a jami'ar tarayya ta Dutse ya laburta cewa wannan ba karamin abin takaici ne saboda yana illata rayuwar daliban jami'o'in Najeriya.

Kara karanta wannan

Na Yi Matuƙar Takaicin Yadda Daliget Ɗin Jihar Mu Ba Su Zaɓe Ni Ba, Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa Na PDP

Yace:

"Duk laifin ASUU da gwamnatin tarayya ne. Gwamnati kuwa ko ajikinsu saboda 'yayansu ba su karatu a makarantun gwamnati."

Ya kara cewa shi dai tun lokacin da ASUU ta tafi yajin aiki ya mayar da hankali kan sana'arsa kuma ya fara neman aikin wucin gadi.

Wani dalibin kuwa, Bashr Ishaq, dan aji daya a jami'ar tarayya dake Abuja yace wannan ba karamin abin kunya bane.

Yace:

"Wannan abin kunya ne ga gwamnati amma muna addu'a yazo karshe. Yanzu dai ina karatu na kuma ina aiki."

Asali: Legit.ng

Online view pixel