Kisan Deborah: Kungiya ta nemi a kamo limamin BUK bisa zargin halasta jinin Bishop Kukah
- Kungiyar kare hakkin bil'adama ta HURIWA ta fusata, ta nemi a gaggauta kama wani limamin Juma'a a jihar Kano
- Wannan ya faro ne daga maganganun da kungiyar ke zargin malamin ya furta kan kisan daliba a kwalejin Sokoto
- Ana ci gaba da kai ruwa rana game da kisa da kone Deborah tare da neman kwato wadanda aka kama a jihar Sokoto
Najeriya - Kungiyar kare hakkin bil’adama ta HURIWA, a ranar Litinin, ta nemi jami'an SSS da su kama babban limamin Jami’ar Bayero Kano, Sheikh Abubakar Jibril bisa zargin tunzura al’ummar Musulmi kan Bishop Matthew Hassan-Kukah.
HURIWA, a cikin wata sanarwa da kodinetan kungiyar na kasa, Emmanuel Onwubiko, ya fitar, ta ce an ga Jibril a wani faifan bidiyo da ake zargin yana gaya wa dimbin mabiyansa musulmi da su nemi adireshin gidan Kukah, kuma su far masa, rahoton Punch.
A ranar Alhamis din da ta gabata ne wasu suka yi wa wata dalibar Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari da ke Sokoto ruwan duwatsu tare da kona gawarta saboda durawa Annabi Muhammad SAW ashariya.
‘Yan sanda sun kama wasu mutane biyu da ake zargi da aikata kisan, inda wasu masu zanga-zanga a ranar Asabar suka bukaci a sake su.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Bukatar da HURIWA ta gabatar
Kungiyar, a cikin sanarwar ta a ranar Litinin, ta zargi Jibril da daukar nauyin harin da aka kai a cocin Kukah ta hanyar fadin kalamai masu tada zaune tsaye a shafukan sada zumunta, inji The Nation.
Onwubiko na HURIWA ya ce:
“A bisa wannan bayanin, HURIWA tana kira ga hukumar tsaro ta farin kaya ta sanar da cewa tana tuhumar Sheikh Abubakar Jibril kan mumunar harin da ’yan daba suka kai a cocin Kukah ranar Asabar."
Tirkashi: Lauyoyi 34 a gaban kotu don kare daliban da suka kashe wacce ta zagi Annabi
A wani labarin, rundunar ‘yan sanda ta gurfanar da wasu mutane biyu da ake zargi da hannu a kisan dalibar Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari da ke Sokoto, Deborah Samuel, da ta durawa Annabi ashariya.
Wadanda ake zargin – Bilyaminu Aliyu da Aminu Hukunchi – wadanda kuma daliban kwalejin ne, an gurfanar da su a gaban wata kotun majistare da ke jihar a ranar Litinin, Daily Trust ta ruwaito.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya bayar da rahoton cewa lauyoyi 34 ne suka bayyana domin kare daliban biyu da ake zargi da kashe dalibar da ta zagi Annabi, inji rahoton Sahara Repoerters.
Asali: Legit.ng