Rikici yayin da jami'in gidan yari ya bindige dan kasuwa akan karan taba sigari a Kano
- Rahoton da muke samu daga majiya a jihar Kano ya bayyana yadda jami'in tsaro ya bindige wani dan kasuwa
- Rahoton ya ce, fada ce ta kaure tsakanin jami'in na gidan yari da dan kasuwa akan karan taba sigari
- Hakazalika, an ce jami'in tsaro ya kwankwadi kwayoyi ne kafin aikata wannan mummunan aiki mai ban takaici
Jihar Kano - Wani jami'in gidan yari dauke da makami da ke aiki da gidan yarin Goron Dutse a jihar Kano ya tafka kuskure, inda ya harbe wani dan kasuwa har lahira bayan wata zazzafar musayar yawu.
Jami'in gidan yarin mai suna Adamu, ana zargin ya harbe dan kasuwar ne bayan wata takadama tsakaninsa da dan kasuwan kan taba sigari.
An tabbatar da mutuwar dan kasuwar a lokacin da aka kai shi asibiti, inji rahoton Sahelian Times.
A cewar wani ganau, Adamu ya tunkari dan kasuwar ne da N200 domin ya siya taba kan naira 10 kowanne.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
A cewarsa:
"Dan kasuwan ya ki sayar da sigarin ga jami'in gidan yarin, nan da nan ya harbe shi sau biyu a ciki."
A cewar majiyar, jami'in ya kuma harbi wani mutum da ke wucewa wurin a kan keke.
Ya kara da cewa Adamu ya kwankwadi miyagun kwayoyi lokacin da ya isa wurin.
Hakazalika, jaridar Aminiya ta ce ta tattaro daga shaidu cewa, alamu sun nuna dan kasuwan na bin jami'in bashi ne, wanda ya hana shi ninka bashin har ta kai ga baceceniya.
Yan bindiga sun harbe mutum 6 har lahira a Kano, sun sace Basarake
A wani labarin, wasu yan bindiga da ake tsammanin masu garkuwa ne sun halaka mutum Shida a wani ƙauyen ƙaramar hukumar Takai, a jihar Kano, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.
Takai na yankin kudancin Kano kuma ta na da nisan kilo mita 80 daga cikin kwaryar birnin Kano kuma ta haɗa iyaka da wasu garuruwa a jihar Jigawa.
Yan bindigan sun farmaki ƙauyen Ƙarfi da ke yankin karamar hukumar Takai kuma suka yi awon gaba da magajin garin ɗan kimanin shekara 53, Abdulyahyah Ilo.
Asali: Legit.ng