Da Dumi-Dumi: Yan bindiga sun cinna wuta a Kamfanin raba wutar Lantarkin Enugu

Da Dumi-Dumi: Yan bindiga sun cinna wuta a Kamfanin raba wutar Lantarkin Enugu

  • Wasu yan bindiga sun banka wuta a kamfanin rarraba wutar Lantarki EEDC da ke jihar Anambra, sun ɓarnata muhimman kayayyaki
  • Jami'in hulɗa da jama'a na EEDC, Mista Emeka Ezeh, ya ce jami'an kashe wuta ba su kawo ɗauki ba har sai da Kwamishina ya sa baki
  • Ya ce sun sanar da hukumomin da ya kamata kuma ba su fatan haka ta sake faruwa nan gaba

Anambra - Wasu mahara da ba'a gane ko su waye ba sun cinna wuta a Ofishin rarraba wutar lantarki na jihar Enugu da ke Ogidi, a Anambra da safiyar ranar Litinin.

Wakilin jaridar Punch ya tattaro cewa kusan kayayyaki masu amfani da Motoci 32 ne suka kone yayin harin.

Maharan sun farmakin ofishin wutar EEDC ne jim kaɗan bayan makamancin haka ta faru a Sakatariyar ƙaramar hukumar Idemili, inda wata Kotun Majistire ke ciki, duk suka haɗa suka kone su.

Kara karanta wannan

2023: Kotu ta aika dan takarar gwamna na PDP gidan gyara hali

Kamfanin raba wuta EEDC.
Da Dumi-Dumi: Yan bindiga sun cinna wuta a Kamfanin raba wutar Lantarkin Enugu Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, shugaban sashin hulɗa da jama'a na EEDC, Mista Emeka Ezeh, ya bayyana damuwarsa cewa duk kokarin sanar da hukumar kashe gobara ta Anambra bai haifar da sakamako mai kyau ba.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ezeh ya ce ma'aikaan Kamfanin, waɗan da ke wurin lokacin da abun ya faru, tilas suka zuba ido kayayyakin wurin na ƙonewa saboda babu wanda ya kawo musu ɗauki da taimako.

Vanguard ta rahoto Ya ce:

"Har sai bayan da kwamishinan abubuwa masu amfani, Mista Julius Chukwuemeka, ya shiga tsakani da misalin ƙarfe 9:05 na safe ya kawo jami'an kashe gobara wurin."

Wane mataki hukumomi suka ɗauka?

Ya ƙara da cewa wannan babban rashi ne a Kamfanin EEDC kuma koma baya a yunkurin da kamfanin yake na inganta alaƙarsa da kwastomomi a Ogidi da Anambra baki ɗaya.

Kara karanta wannan

Zanga-zanga bayan zagin Annabi: Tambuwal ya sassauta dokar hana fita a Sokoto

"Tuni muka jawo hankalin hukumomin da suka dace kuma muna tsammanin zasu gudanar da bincike domin kamo masu hannu a lamarin su girbi abinda suka shuka."
"Babu ta yadda tattalin arziki kamar na mu zai cigaba matuƙar za'a cigaba da samun irin haka. Mungode Allah ba wanda ya mutu sanadin lamarin, kuma mun yi Allah wadai tare da addu'ar Allah ya kiyaye gaba."

A wani labarin na daban kuma Yan bindiga sun kai mummunan hari Sakatariyar ƙaramar hukuma, sun aikata ta'asa mai yawa

Wasu tsagerun yan bindiga sun kone ƙaramar hukuma guda da wata Kotun Majistire a jihar Anambra da daren jiya Lahadi.

Wata majiya ta ce maharan sun kona fayil-fayin da kadarorin da ke cikin harabar wurin ciki har da motocin da aka aje.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262