Yan bindiga sun yi kaca-kaca da Sakatariyar ƙaramar hukuma da Kotu a Anambra

Yan bindiga sun yi kaca-kaca da Sakatariyar ƙaramar hukuma da Kotu a Anambra

  • Wasu tsagerun yan bindiga sun kone ƙaramar hukuma guda da wata Kotun Majistire a jihar Anambra da daren jiya Lahadi
  • Wata majiya ta ce maharan sun kona fayil-fayin da kadarorin da ke cikin harabar wurin ciki har da motocin da aka aje
  • Kakakin rundunar yan sandan jihar ya ce tuni yan sanda suka shawo kan lamarin kuma an kashe wutar baki ɗaya

Anambra - Wasu da ake zargin yan bindiga ne sun ƙona Sakatariyar ƙaramar hukumar Indemili da kuma wata Kotun Majirtire da ke cikin harabar wurin.

Wata majiya ta shaida wa Punch cewa maharan sun farmaki harabar sakatariyar ne ranar Lahadi da daddare kuma suka aikata wannan ta'adi.

Bayanai sun nuna cewa yan bindigan sun ƙone fayil-fayil da wasu kadarori a wurin, har da ginin Sakatariyar.

Wurin da yan bindiga suka kai hari.
Yan bindiga sun yi kaca-kaca da Sakatariyar ƙaramar hukuma da Kotu a Anambra Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Bidiyo da hotunan harin da ke yawo a Intanet sun nuna cewa baki ɗaya Sakatariyar ta kone a harin.

Kara karanta wannan

Babbar Magana: Miyagun 'yan bindiga sun sace ɗan majalisa a mazaɓar da gwamna ya fito

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Haka nan kuma, Motocin da aka aje a harabar Sakatariyar ƙaramar hukumar sun ƙone kurmus sanadin harin na daren Lahadi.

Hukumar yan sanda ta tabbatar

Yayin da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin hukumar yan sanda, DSP Tochukwu Ikenga, ya alaƙanta harin da wasu masu ta da wuta da ba'a gano ba.

A kalamansa ya ce:

"Eh, tabbas lamarin ya faru kuma tuni jami'an yan sanda suka dura wurin domin dawo da komai dai-dai."
"A halin yanzun, an kashe wutar baki ɗaya ta daina ci, kuma zaman lafiya a yankin ya dawo kamar yadda ya ke a baya."

Yan bindiga sun kashe sojoji 2

Kazalika a wani cigaban kuma, wasu miyagu sun halaka Sojoji biyu a wata musayar wuta da suka yi a 3-3 estate, Nkwelle Ezunaka, kusa da Onitsha, a jihar Anambra ranar Lahadi da daddare.

Kara karanta wannan

Bayan Debora a Sokoto, wata Naomi Goni ta sake kalaman batanci ga Annabi SAW a Borno

Wani mazaunin Anguwar, wanda ya nemi a ɓoye bayanansa, ya tabbatar da cewa yan bindiga sun harbe sojoji biyu har lahira yayin harin.

A cewarsa, sun fara gumurzun ne da misalin ƙarfe 10:00 na safe kuma sun kwashe awanni. Bayanai sun nuna maharan sun farmaki dakarun soji ne waɗan da ke zaune a jerin gidajen.

Wata majiya ta shaida wa Daily Trust cewa:

"Eh gaskiya ne, jiya a babbar Kofar shiga Anguwar Estate, yan bindiga sun farmaki sojojin da ke tsare mu da ƙarfe 10:00 na dare. Sojoji biyu sun rasa rayuwarsu."

A wani labarin kuma Jami'an tsaro sun ɗauki mataki bayan wata Kirista ta sake kalaman Batanci ga Annabi a Borno

Yayin da aka fara jitar-jitar wata kirista ta sake kalaman batanci ga Annabi, Jami'an tsaro sun shirya ba da tsaro a birnin Maiduguri.

Rahoto ya nuna cewa wacce ake zargi da yin ɓatancin ta taɓa zama a jihar Borno, amma ta jima da barin jihar.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: 'Yan bindiga sun kashe mutum 1, sun yi garkuwa da wasu 20 a Kaduna

Asali: Legit.ng

Online view pixel