Jami'an tsaro sun ɗauki mataki bayan wata Kirista ta sake kalaman Batanci ga Annabi a Borno

Jami'an tsaro sun ɗauki mataki bayan wata Kirista ta sake kalaman Batanci ga Annabi a Borno

  • Yayin da aka fara jitar-jitar wata kirista ta sake kalaman batanci ga Annabi, Jami'an tsaro sun shirya ba da tsaro a birnin Maiduguri
  • Rahoto ya nuna cewa wacce ake zargi da yin ɓatancin ta taɓa zama a jihar Borno, amma ta jima da barin jihar
  • Wani masanin tsaro a tafkin Chadi ya ce mazauna musamman matasa sun fusata da lamarin, sun fara shirin zanga-zanga

Borno - Dakarun rundunar sojin Najeriya, yan sanda, jami'an tsaron NSCDC da yan Banga, zasu fara aikin gargaɗi ga mutane a cikin kwaryar birnin Maiduguri, jihar Borno.

The Cable ta gano cewa dakarun tsaron sun kai ga cimma wannan matsaya ne a wani taro da suka gudanar ranar Asabar a Hedkwatar yan sanda ta jihar Borno.

Taron ya samu halartar kwamandan rundunar sojoji ta 7, shugabannin hukumomin tsaro, Malaman addinin Musulunci, shugabannin kiristoci (CAN) da sauran su.

Kara karanta wannan

Tambuwal da 'Yan siyasa 3 da za su shiga zaben 2023 da niyyar takarar kujeru 2 a lokaci 1

Sojojin Najeriya.
Jami'an tsaro sun ɗauki mataki bayan wata Kirista ta sake kalaman Batanci ga Annabi a Borno Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Meyasa zasu ɗauki wannan matakin?

A cewar Zagazola Makama, masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi, jami'ai zasu ɗauki matakin ne sakamakon shirin gudanar da zanga-zanga da matasa ke yi kan zargin wata Kirista ta yi kalaman ɓatanci ga Annabi Muhammad (SAW) a shafinta na Facebook.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Matar mai suna, Naomi Goni, yayin wata muhawara da wani a dandalin Facebook, ta yi kalaman ɓatancin da ka iya ta da zaune tsaye, kuma nan take ya fara yawo a kafafen sada zumunta.

Faruwar hakan ta jawo mazauna jihar da kuma matasa suka fara kiran a gaggauta ɗaukar matakin kan matar da ta yi kalaman.

Sai dai bayanai sun nuna cewa Naomi Goni, ta yi gaggawar zuwa ta goge shafinta baki ɗaya daga dandalin sada zumunta Facebook.

Zagazola ya ce:

"A cewar wata kwakkwaran majiya daga jami'an tsaro wanda ya halarci wurin taron, sun gano cewa Naomi ba ta cikin jihar Borno lokacin da ta yi kalaman, amma ta halarci ɗaya daga cikin makarantun jihar, bayan haka ta jima da barin Borno."

Kara karanta wannan

Dokar kulle: Bishop Kukah ya yabawa matakin Tambuwal, ya karyata batun kai hari gidansa

Masanin ya ƙara da cewa hukumomin tsaro sun yi shirin kwace iko da gidan da Naomi ta yi amfani da shi lokacin da ta zauna Borno domin daƙile abin da ka iya zuwa ya dawo.

A wani labarin kuma Iyayen Ɗalibar da ta zagi Annabi a Sokoto sun yi magana kan kashe ɗiyarsu bayan binne gawarta

Iyayen ɗalibar da ta yi kalaman Batanci ga Annabi Muhammad (SAW) sun yi magana kan abinda ya faru a Sakkawato bayan binne gawarta.

Mahaifin Debora Samuel ya bayyana yadda direbobi suka guje shi kafin ya sami wanda ya ɗakko gawar zuwa Neja kan N120,000.

Asali: Legit.ng

Online view pixel