Doka a hannu: Tashin hankali yayin da 'yan acaba suka kashe tare da kone wani akan N100

Doka a hannu: Tashin hankali yayin da 'yan acaba suka kashe tare da kone wani akan N100

  • An samu tashin tashina a wani yankin jihar Legas yayin da wasu 'yan acaba suka bankawa wani matashi wuta
  • Wannan lamari ya jawo cece-kuce a kafafen sada zumunta, inda wasu ke neman a gaggauta daukar mataki kan 'yan acaban
  • Rahoton da muka samu daga tushe ya bayyana yadda lamarin ya faru har 'yan acaban suka fusata suka dauki doka a hannu

Legas - ‘Yan Najeriya sun bukaci a nemawa wani injiniyan sauti mai suna David adalci, wanda wasu da ake zargin 'yan acaba ne suka yi masa duka tare da kona shi a unguwar Admiralty da ke Lekki a jihar Legas.

Punch Metro ta tattaro cewa abokan aikin injiniyan, Frank da Philip sun hau acaba zuwa wani wurin da ke Admiralty Way, Lekki, inda David ke shirya wasan kwaikwayo.

Kara karanta wannan

Sheikh Gumi: An Sha 'Zagin' Annabi Lokacin Yana Raye, Amma Bai Kashe Kowa Ba Saboda Hakan

Yadda aka kone wani akan N100
Doka a hannu: Tashin hankali yayin da 'yan acaba suka kashe tare da kone wani akan N100 | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

An ce dan acaban ya kai mutanen biyu ne zuwa inda aka nufa sai kawai wata takaddama ta kaure kan N100 tsakanin dan acaban da abokan David.

An ce gardamar ta rikide zuwa fada, inda dan acaban ya nemi taimakon wasu 'yan acaba, wadanda suka shiga lamarin.

A yayin shiga tsakani, an ce 'yan acaban sun kai wa Frank da Philip hari lokacin da aka sanar da David lamarin.

A kokarin ceto abokansa, Dauda ya fice daga wurin taron.

Amma yayin da ya isa wurin abokan nasa, ana zargin 'yan acaban sun kama shi tare da lakada masa duka har sai da ya suma.

Yayin da Dauda ke kwance babu motsi a kasa, an ce maharan sun zuba masa mai suka banka masa wuta.

Wasu shaidun gani da ido sun dauki faifan bidiyo na abin da 'yan acaban suka yi a wurin.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: 'Yan bindiga sun kashe mutum 1, sun yi garkuwa da wasu 20 a Kaduna

An fitar da faifan bidiyon a yanar gizo yayin da ‘yan Najeriya da ‘yan uwa da abokan arziki suka fusata suka bukaci a dauki mataki, kamar yadda SaharaReporters ta tattaro.

Zagin Annabi a Sokoto: Masu zanga-zanga sun farmaka tare da lalata coci 2 a Sokoto

A wani labarin, wasu matasa masu zanga-zanga a ranar Asabar, 14 ga watan Mayu, sun kona tare da lalata wasu coci biyu karkashin jagorancin Bishop din darikar Katolika na Sokoto, Matthew Hassan-Kukah.

Rabaran Christopher Omotosho, daraktan hulda da jama’a na cocin Katolika na Sokoto ne ya tabbatar da faruwar lamarin, inji rahoton jaridar The Punch.

Omotosho ya bayyana cewa fusatattun matasan sun kona kofar daya daga cikin gine-ginen cocin tare da kona wata mota bas a harabarsa. Ya kara da cewa sun kuma lalata coci na biyu da lamarin ya shafa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.