Abin da ya sa har yau mu ka gagara kawo karshen yajin-aikin ASUU Inji Ministan Buhari
- Ministan kwadago, Festus Keyamo ya ce akwai inda ASUU ke da gaskiya a rikicinta da Gwamnati
- Shi ma Chukwuemeka Nwajiuba ya nemi afuwar daliban Najeriya a game da rufe jami’o’in da aka yi
- Nwajiuba ya ce yajin-aikin da kungiyar ASUU ta shiga ya taba shi domin ‘ya ‘yansa biyu su na zaune a gida
Kwara - Karamin Ministan kwadago na kasa, Festus Keyamo ya yi bayanin abin da ya sa yake da wahala gwamnatin tarayya da ASUU ta iya cin ma matsaya.
Da yake jawabi a wajen wani taro da aka shirya a cibiyar MINILS da ke garin Ilorin, Daily Trust ta ce Keyamo ya zargi yajin-aikin da jagwagwala harkar ilmi.
Ministan ya bayyana cewa sabanin da ake samu da kungiyar kwadago yana da wahalar sha’ani, kuma yana bukatar ilmi da sanin aiki kafin a shawo kan shi.
“Matsalolin da aka samu a nan biyu ne, sabanin fahimta da neman hakki. Daga cikin abin da nake goyon bayan ASUU shi ne rashin kara masu albashi.”
“Abin kunya ne Farfesa ya rika karbar N350, 000 a matsayin albashi duk wata. Duk da kuwa mafi karancin albashi yana aiki ne ga kananan ma’aikata.”
“Asalin rikicin shi ne tsakanin ASUU da ma’aikatar ilmi. Sabani a kan dawainiyar ilmi. A nan akwai bukatar a nemi maslahar da ba yajin-aiki ba.”
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Festus Keyamo SAN
A cewar Ministan ta bakin Darekta Janar na MINILS, Kwamred Isa Aremu, rufe jami’o’i na wata da watanni da sunan ana yajin-aiki ya nakasa harkar ilmi.
Ayi hakuri - Chukwuemeka Nwajiuba
A gefe guda, The Cable ta rahoto tsohon Ministan ilmi, Chukwuemeka Nwajiuba yana ba dalibai hakuri saboda bai iya sa an daina yajin-aiki da yake ofis ba.
Da aka yi hira da shi a gidan talabijin, Nwajiuba ya shaida cewa akwai ‘ya ‘yansa biyu da ke karatu a jami’o’in gwamnati da yaji-aikin ASUU ya shafe su.
Tsohon Ministan ya ce duka ‘ya ‘yansa hudu sun je jami’an gwamnati, ya kuma ce ASUU ta na kokarin kawo gyara ne a ilmi, amma dole a fahimci lamarin.
Ba za mu koma aiki ba sai... - ASUU
A makon jiya, mun kawo rahoto da ya nuna cewa kungiyar malaman jami'o'i na ASUU ba za ta janye yajin-aikinta ba sai gwamnati ta cika duk sharudanta.
An yi zama da malaman jami’ar a fadar Aso Rock Villa da nufin ganin an bude jami’o’in Najeriya. A karshe zaman da aka yi da ASUU bai haifar da ‘da mai ido ba.
Asali: Legit.ng