Atiku: Dalilin da yasa na goge rubutun Alla-wadai da kashe wacce ta zagi Annabi a Sokoto

Atiku: Dalilin da yasa na goge rubutun Alla-wadai da kashe wacce ta zagi Annabi a Sokoto

  • Dan takarar shugaban kasa a PDP, Atiku Abubakar ya bayyana dalilin da yasa ya goge sakon da aka wallafa a shafinsa na Twitter
  • Atiku ya bayyana cewa, babu sakon da ake wallafawa a shafinsa face sai ya samu amincewa daga gareshi
  • Sakon da aka yadan dai ya haifar da cece-kuce da yawa a shafukan sada zumuntan Najeriya tun farko

Najeriya - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Abubakar Atiku, ya ce dole ne duk wani sakon Twitter da ke shafinsa ya samu amincewarsa kafin a yada shi a duniya.

A baya Abubakar ya mayar da martani game da kisan Deborah Samuel da aka zarga da aikata mummunar dabi'ar batanci ga Annabi SAW, inji rahoton Leadership.

Ba da daɗewa ba aka goge sakon, wanda ya haifar da cece-kuce a kafofin watsa labarun kasar nan.

Kara karanta wannan

Deborah Samuel: Ƴan Najeriya Sun Yi Wa Ɗan Tsohon IGP Martani Kan Kalamansa Game Da Kisar Ɗalibar Sokoto Da Ta Zagi Annabi

Atiku ya magantu kan sakon Twitter na Alla-wadai da kashe Deborah
Atiku: Dalilin da yasa na goge rubutun Alla-wadai da kashe wacce zagi Annabi a Sokoto | Hoto: thenationonlineng.net
Asali: Twitter

Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP ya bayyana dalilin doge sakon ne a lokacin da ya kai ziyarar neman goyon baya ga Gwamna Godwin Obaseki na Edo a gidan gwamnati da ke Benin, kamar yadda Channels Tv ta ruwaito.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Yace:

"Kowane rubutun Twitter dole ne ya sami amincewa ta amma wannan bai samu ba don haka na nemi su sauke shi.
“Na tsaya tsayin daka game da shari’ar Musulunci, aka zage ni, aka jefe ni da duwatsu, amma har yaushe hakan ya kare? Duk da haka, ban canza matsayina a kan hakan ba. Ba na jin tsoron tsayawa kan batutuwa masu mahimmanci."

Zagin Annabi a Sokoto: Masu zanga-zanga sun farmaka tare da lalata coci 2 a Sokoto

A wani labarin, wasu matasa masu zanga-zanga a ranar Asabar, 14 ga watan Mayu, sun kona tare da lalata wasu coci biyu karkashin jagorancin Bishop din darikar Katolika na Sokoto, Matthew Hassan-Kukah.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Ministan Buhari Da Ya Yi Murabus Don Takarar Gwamna Ya Janye Takararsa

Rabaran Christopher Omotosho, daraktan hulda da jama’a na cocin Katolika na Sokoto ne ya tabbatar da faruwar lamarin, inji rahoton jaridar The Punch.

Omotosho ya bayyana cewa fusatattun matasan sun kona kofar daya daga cikin gine-ginen cocin tare da kona wata mota bas a harabarsa. Ya kara da cewa sun kuma lalata coci na biyu da lamarin ya shafa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.