Abin da Malamai suka faɗa wa gwamna Tambuwal a wurin taron bayan kashe ɗalibar da ta zagi Annabi a Sokoto

Abin da Malamai suka faɗa wa gwamna Tambuwal a wurin taron bayan kashe ɗalibar da ta zagi Annabi a Sokoto

  • Malaman da suka halarci taro da gwamna Tambuwal sun shawarci gwamnati kan yadda za'a dakile faruwar ɗaukar doka a hannu nan gaba
  • Gwamnan ya kira taro da Malamai ne bayan rikicin da ya yi sanadin kashe ɗaliba da ake zargin ta yi batanci ga Annabi SAW
  • Mutane sun fito zanga-zanga inda suka bukaci a saki waɗan da aka kama da zargin kashe ɗalibar

Sokoto - Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokoto ya kira taron gaggawa da Malaman masallatan Jumu'a na jihar biyo bayan kashe ɗalibar da ta zagi Annabi.

A ranar Lahadi, Daily Trust ta rahoto cewa Malaman da suka halarci taron sun shawarci gwamnati a matakin ƙasa da jiha ta samar doka wacce zata haramta ɓatanci a kasar nan.

Bayanai sun nuna cewa Malaman sun fito fili sun shaida wa gwamnan cewa matuƙar ba'a samar da doka tare da tsattsauran hukunci ba to jama'a zasu cigaba da ɗaukar doka a hannu.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Bidiyon Kwankwaso Ya Isa Gidan Shekarau Don 'Ƙarasa' Maganan Komawarsa NNPP

Masu zanga-zanga a Sokoto.
Abin da Malamai suka faɗa wa gwamna Tambuwal a wurin taron bayan kashe ɗalibar da ta zagi Annabi a Sokoto Hoto: ogbomoso tv/facebook
Asali: Facebook

Ɗaya daga cikin Malaman da suka halarci taron ya ce Malamai sun ba da shawara cewa ya dace a kafa doka mai ɗauke da hukunci kamar kisa ga duk wanda ya karyata.

A cewarsu, hakan ne kaɗai zai hana mutane yin kalaman ɓatanci ga wani addini ko wani Mutum mai daraja a Addini.

Hakanan sun shawarci gwamnati ta sanya doka cewa wajibi kowane ɗalibi da aka ba gurbin karatu ya yi rantsuwa zai girmama Addinin abokanan karatunsa.

An kashe mutum ɗaya wajen zanga-zanga

Aƙalla mutum ɗaya ya rasa rayuwarsa yayin da wasu suka jikkata a kokarin jami'an tsaro na kwantar da zanga-zangar da ta ɓarke a Sakkwato bayan kashe Debora.

Mutane sun fantsama kan tituna a Sakkwato ranar Asabar inda suka nemi hukumomi su sako waɗan da suka kama da zargin kashe wacce ta yi ɓatanci ga Annabi (SAW).

Kara karanta wannan

Na rantse babu wanda zai saci ko kwabo idan na zama shugaban kasa, Atiku

A ranar Alhamis, wata ɗalibar kwalejin Shehu Shagari mai suna, Debora Samuel, ta rasa rayuwarta a hannun ɗalibai yan uwanta bisa zargin ta yi kalaman ɓatanci.

Waɗan da suka fito zanga-zangar sun ɗaga alluna ɗauke da rubutun, "A sako yan uwan mu," "Musulmai ba yan ta'adda bane," da sauran su.

Da farko an fara zanga-zangar cikin lumana amma daga baya adadin mutane ya ƙaru, wasu kan ababen hawa suna kiran Allahu Akbar.

A wani labarin na daban kuma Dirama a Kano yayin da tawagar Kwankwaso ta dira gidan Shekarau awanni bayan tafiyar Ganduje

Siyasar Kano ta ƙara rikicewa musamman tsakanin gwamna Abdullahi Umar Ganduje da Sanata Ibrahim Shekarau.

Bayan ziyarar Ganduje gidan Shekarau don hana shi komawa NNPP, Kwankwaso ya tura tawaga kafin zuwansa gidan Shekarau.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262