Zagin Annabi: Gwamnatin Sokoto ta dakatar da komawa makarantu, ta kara mako guda

Zagin Annabi: Gwamnatin Sokoto ta dakatar da komawa makarantu, ta kara mako guda

  • Gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal ya dakatar da shirin komawa makaranta da ya kamata ayi a wannan makon
  • Hakan ya kasance ne sakamakon dokar kulle da aka saka a jihar biyo bayan kisar Deborah Samuel, wacce matasa suka yi kan batanci ga Annabi (SAW)
  • Sai dai wannan bai shafi daliban ajin karshe da za su fara zana jarrabawar WAEC daga ranar Litinin, 16 ga watan Mayu ba

Sokoto - Gwamnatin jihar Sokoto ta sanar da dakatar da shirin komawa makarantun Firamare da na Sakandare a jihar, ta kara mako guda a kan hutun.

Kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) ta rahoto cewa ya kamata makarantu su koma ajujuwa a wannan makon da za a shiga.

Makarantun kwana za su koma a ranar Lahadi, 15 ga watan Mayu, sannan na jeka ka dawo za su koma a ranar Litinin, 16 ga watan Mayu.

Kara karanta wannan

Zagin Annabi a Sokoto: Masu zanga-zanga sun farmaka tare da lalata coci 2 a Sokoto

Zagin Annabi: Gwamnatin Sokoto ta dakatar da komawa makarantu, ta kara mako guda
Zagin Annabi: Gwamnatin Sokoto ta dakatar da komawa makarantu, ta kara mako guda Hoto: Premium Times
Asali: Facebook

Batun dakatarwar na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga kakakin ma’aikatar makarantun firamare da sakandare a ranar Lahadi, a garin Sokoto, Premium Times ta rahoto.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An tattaro cewa dakatarwar ya biyo bayan dokar hana fita ta sa’o’i 24 da gwamnati ta ayyana.

Ya kara da cewar kwamishinan ma’aikatar firamare da sakadare din, Bello Guiwa, ya umurci dukkan makarantun gwamnati da masu zaman kansu da su koma a ranar 22 da 23 ga watan Mayu.

“Sai dai, abun bai shafi daliban ajin karshe da ya kamata su fara rubuta jarrabawar WAEC ba a ranar Litinin, 16 ga watan Mayun 2023.
“Ana sanya ran iyaye, malamai, SBMC da PTA da su bi umurnin dan Allah.”

A wani lamari makamancin haka, an shawarci masu bautan kasa a jihar Sokoto musamman wadanda ke zaune a cikin kuryar garin Sokoto da su kasance a gida saboda dokar kulle na awa 24, jaridar Independent ta rahoto.

Kara karanta wannan

A zauna lafiya: Gamayyar gwamnonin Arewa sun yi Alla-wadai da kashe dalibar da ta zagi Annabi

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa daga kakakin shirin a jihar Sokoto, Sani Idris, a ranar Lahadi a Sokoto.

Ya ce hukumar gudanarwar shirin ta tuntubi dukkan hukumomin tsaro, domin tabbatar da tsaron lafiyar yan bautar kasar a duk tsawon lokacin dokar hana fitar da sauran su.

Dokar kulle: Bishop Kukah ya yabawa matakin Tambuwal, ya karyata batun kai hari gidansa

A wani labarin, babban Limamin Cocin Katolika na Diocese na Sokoto, Mathew Kukah, ya yabawa gwamnan jihar, Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal kan ayyana dokar kulle na awa 24 da ya gaggauta yi domin kwantar da zanga-zangar da ke gudana a jihar, rahoton Vanguard.

Da farko masu zanga-zangar sun farmaki cocin Holy Family Catholic Cathedral a hanyar Bello Road da St. Kevin’s Catholic Church, Gidan Dere, inda suka faffasa wunduna da wata tashar mota a harabar.

Idan za ku tuna gwamnan ya shirya zuwa jihohi shida don tuntubar da ke gudana kan kudirinsa na son takarar shugaban kasa. Sai dai kuma, ya soke tafiyar don tabbatar da dawo da zaman lafiya a jihar.

Kara karanta wannan

Dokar kulle: Bishop Kukah ya yabawa matakin Tambuwal, ya karyata batun kai hari gidansa

Asali: Legit.ng

Online view pixel