'Yan bindiga sun kai wasika Zamfara bayan kashe manoma 7 da Limamin masallacin Juma'a

'Yan bindiga sun kai wasika Zamfara bayan kashe manoma 7 da Limamin masallacin Juma'a

  • Wasu 'yan bindiga sun kai mummunan hari jihar Zamfara, sun hallaka mutane bakwai tare wani limamin masallacin Juma'a
  • Wannan na zuwa ne daidai lokacin da manoma ayankin ke fara sharar gona a shirye-shiryen daminan bana
  • 'Yan bindigan sun kuma mika wasika ga wani hakimin yankin domin sanar da mazauna biyan haraji da fansan manoma

Zamfara - Wasu ‘yan ta’adda sun kashe akalla manoma 7 da babban limamin masallacin Juma’a na garin Faru mai suna Malam Sani Akwala a ranar Asabar, a kauyen Dajin Danau da ke kauyen Faru a karamar hukumar Maradun a jihar Zamfara.

An kai harin ne da misalin karfe 12:45 na rana lokacin da 'yan ta'adda kusan 30 dauke da makamai suka kai farmaki a gonakin da ke Faru, wanda ke da nisan kasa da kilomita daya.

Kara karanta wannan

Ta'addanci: 'Yan ta'adda sun bindige jami'an 'yan sanda har 3 a jihar Neja

‘Yan ta'addan sun hadu da manoman ne a lokacin da suke aikin sassabe a gonakinsu. Da ganinsu, sai wasu manoman suka gudu domin tsira da rayukansu.

'Yan bindiga sun farmaki mazauna, sun hallaka mutum 7 a jihar Zamfara
'Yan bindiga sun kai wasika Zamfara bayan kashe manoma 7 da wani Limami | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Saidu Bala Faru, wani ganau da ya tsallake rijiya da baya, ya shaida wa HumAngle cewa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“Muna gonakinmu saboda an yi ruwan sama kamar da bakin kwarya a jiya (Juma’a), kwatsam sai ga shi wadanan ‘yan ta’adda dauke da makamai sun fara harbin mutanen mu.
“Daga cikin manoma bakwai da aka kashe yayin harin akwai Sani Abdullahi, Muhammad Mani Na-Umma, Mala, Sani Na-Akwala, da Muhammad Lauwali Yar-Tusgi.”

Adnan Katara, wani manomi, ya ce:

“Dukkan mutanen bakwai da aka kashe, shugabannin gidajensu ne… sun bar yara sama da 49 a matsayin marayu da za su tagayyara a kauyen.”

Yadda aka farmaki kauye da sunan neman kudin fansan noma

Kara karanta wannan

Sokoto: Bishop Kukah ya yi martani kan kashe dalibar da ta yi batanci ga Annabi

Ibrahim Isah ya ci gaba da shaida wa HumAngle cewa ’yan bindigan sun afkawa kauyukan da ke karkashin gundumar Faru suna neman kudin fansa kan ayyukan noma a yankunan.

A wata wasika da kungiyar ta’addancin ta rubuta kuma ta kai wa hakimin kauyen, ‘yan ta’addan sun ce:

“Babu wani aikin noma da za a yi a yankin a lokacin damunan bana har sai an cimma matsaya kan harajin noma.”

Isah ya kara da cewa:

"Kungiyar ta'addancin na zagayawa gonaki-gonaki domin tabbatar da bin umarninsu."

Ya koka da cewa zai yi wahala manoma a wannan daminar su yi noma, ya kuma yi kira ga hukumomi da su gaggauta yin wani abu.

Kokarin jin ta bakin mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara, SP Mohammed Shehu ya ci tura saboda ba a iya samunsa ta wayar tarho ba.

Ta'addanci: 'Yan ta'adda sun bindige jami'an 'yan sanda har 3 a jihar Neja

Kara karanta wannan

Iftila'i: An tafka ruwan sama a Damaturu, ya rusa gidaje, ya hallaka mutane 5

A wani labarin, wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kashe ‘yan sanda uku da wani direban babur a garin Suleja na jihar Neja.

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 11 na daren ranar Alhamis.

Rahotanni sun ce ‘yan sandan sun amsa kiran gaggawa ne a lokacin da aka yi musu kwanton bauna a kusa da wani wuri da ake kira Old Barracks.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.