Abj-Kad: 'Yan bindiga sun sako mata mai cikin da suka sace a harin jirgin kasa

Abj-Kad: 'Yan bindiga sun sako mata mai cikin da suka sace a harin jirgin kasa

  • 'Yan ta'addan da suka kai hari kan jirgin Abuja zuwa Kaduna sun sako wata mata mai juna biyu da suka sace
  • Wannan na zuwa ne watanni bayan da 'yan ta'addan suka sace fasinjoji da dama a wani jirgin kasan Abuja
  • Har yanzu akwai sauran jama'ar da ke hannun 'yan ta'addan da ke jiran tsammanin ceto daga jami'an tsaro

Kaduna - Wasu da ake zargin ‘yan ta’addan Ansaru ne da suka kai harin nakiya a jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna tare da yin garkuwa da fasinjoji da dama sun sako wata fasinja mai juna biyu.

A cikin wani faifan bidiyo da Daily Nigerian ta samu, matar ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta tattauna da ‘yan ta’addan domin ceto rayukan wasu da ke tare da su.

Kara karanta wannan

Ta'addanci: 'Yan ta'adda sun bindige jami'an 'yan sanda har 3 a jihar Neja

Harin 'yan bindiga a Kaduna: An sako mata mai juna biyu
Abj-Kad: 'Yan bindiga sun sako mata mai cikin da suka sace a harin jirgin kasa | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Ta ce wadanda suka yi garkuwa da su na kula da su, suna ciyar da su da kyau har ma da ba su magunguna.

An ruwaito daga majiyar tsaro cewa ba a biya kudin fansa ba domin a sako ta, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Majiyar ta kuma yi watsi da rahotannin da ke cewa wata mata ta haihu a hannun ‘yan ta’addan.

Gwamnatin Tarayya ta yi alkawarin sakin fasinjoji sama da 60 da aka yi garkuwa da su a ranar 28 ga Maris, 2022, amma har yanzu yawancinsu suna hannunsu.

An bayar da rahoton cewa an sako mutum biyu bayan makudan kudin fansa.

Wadanda aka sako - Manajan Daraktan Bankin Noma, Alwan Hassan da dan kungiyar Dattawan Arewa, Farfesa Ango Abdullahi, sun shafe makonni a hannunsu.

‘Yan uwan ​​sauran fasinjojin da suka rage a sansanin ‘yan ta’adda sun yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta yi kokari saki ‘yan uwansu.

Kara karanta wannan

Rokon da Shugaba Buhari ya yi, ya fada a kan kunnen kashi, ASUU ta cigaba da yajin-aiki

Ta'addanci: 'Yan ta'adda sun bindige jami'an 'yan sanda har 3 a jihar Neja

A wani labarin, wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kashe ‘yan sanda uku da wani direban babur a garin Suleja na jihar Neja.

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 11 na daren ranar Alhamis.

Rahotanni sun ce ‘yan sandan sun amsa kiran gaggawa ne a lokacin da aka yi musu kwanton bauna a kusa da wani wuri da ake kira Old Barracks.

Asali: Legit.ng

Online view pixel