'Batanci: Jakadiyar Birtaniya Ta Ce Dole a Hukunta Waɗanda Suka Kashe Ɗaliban Sokoto
- Jakadar Birtaniya a Najeriya, Catriona Laing, ta yi alla wadai da kisar dalibar Kwalejin Ilimi a Sokoto, Deborah Samuel
- Fusatatun dalibai sun kashe Deborah ne kan zarginta da furta kalamai na batanci ga Annabi Muhammadu (SAW)
- Laing, ta bukaci yan sanda da sauran hukumomin da abin ya shafa su tabbatar sun hukunta wadanda suka aikata abin
Catriona Laing, Jakadar Birtaniya a Najeriya, ta yi alla wadai da kashe Deborah Samuel, wata dalibar Kwalejin Shehu Shagari da ke Jihar Sokoto,kamar yadda ta rubuta a shafinta a Twitter.
Rahotanni sun ce dandazon fusatattun dalibai sun afka wa dalibar ne kan zarginta da furta maganganu na batanci ga Annabi Muhammad (SAW).
Wani bidiyo da ke nuna dalibar ana jifanta da duwatsu da sanduna a shafukan sada zumunta, inda aka ce lamarin ya faru ne a safiyar ranar Alhamis.
Laing ta bukaci mahukunta su tabbatar an hukunta wadanda suka kashe Deborah
A wani wallafa da ta yi a shafinta na Twitter, Laing ta ce ya zama dole mahukunta su tabbatar an hukunta wadanda suka aikata abin.
"Na yi alla wadai da kisan Deborah Samuel a Sokoto, kuma ina kira ga yan sanda da hukumomin da abin ya shafa su tabbatar an hukunta wadanda suka aikta wannan mummuna abin bisa tsarin doka," ta rubuta.
Rundunar yan sanda ta Jihar Sokoto ta ce ta kama mutane biyu kan zarginsu da hannu a kisar dalibar mace.
'Batanci: Atiku Ya Ce Ba Shine Ya Wallafa Rubutun Sukar Kashe Ɗalibar Sokoto a Shafinsa Ba
A bangarensa, Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar PDP ya nisanta kansa daga yin ala-wadai akan kisan Deborah Samuel.
Deborah dalibar aji biyu ce a kwalejin ilimi ta Shehu Shagari da ke Jihar Sokoto, kuma kirista ce, an halaka ta ne bisa zarginta da yin batanci ga Annabi Muhammad SAW.
Sai dai Atiku ya yi wata wallafa a Twitter inda ya ce:
“Babu adalci dangane da kisan muguntar da aka yi mata. An halaka Deborah Yakubu kuma wajibi ne a kwatar mata hakkinta akan wadanda su ka halaka ta. Ina mai yi wa ‘yan uwanta da kawayenta ta’aziyya.”
Asali: Legit.ng