Yanzu-Yanzu: Tambuwal Ya Saka Dokar Hana Fita Ta Awa 24 a Sokoto

Yanzu-Yanzu: Tambuwal Ya Saka Dokar Hana Fita Ta Awa 24 a Sokoto

  • Gwamnan Jihar Sokoto, Mr Aminu Waziri Tambuwal ya saka dokar hana fita na awa 24 na kwana guda a birnin Sokoto
  • Kamar yadda ya sanar a shafinsa na Facebook, an saka dokar ne domin tabbatar da zaman lafiya da bin doka da oda
  • A safiyar yau wasu matasa suka fito zanga-zanga a titunan Sokoto suna neman yan sanda su saki wadanda aka kama kan zargin kisar daliba Deborah Samuel

Jihar Sokoto - Gwamnan Jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal ya saka dokar hana fita ta sa'a 24 a birnin Sokoto, rahoton TVC.

Hakan ya biyo bayan zanga-zanga ne da aka fara yi a wasu sassan birnin ne neman sako matasan da aka kama da kan zargin hannu kisar dalibar kwalejin Ilimi ta Sokoto, Deborah Samuel, wacce ake zargi ta zagi Annabi.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: An saki sakamakon jarabawar JAMB a Najeriya

Yanzu-Yanzu: Tambuwal Ya Saka Dokar Hana Fita Ta Awa 24 a Sokoto
Tambuwal Ya Saka Dokar Hana Fita Ta Awa 24 a Sokoto. Hoto: The Nation.
Asali: Depositphotos

A cewar wata gajeruwar sanarwa da gwamnan ya fitar a shafin gwamnatin Sokoto na Facebook ta hannun hadiminsa na musamman kan watsa labarai, Mohammed Bello, ya ce:

"Domin tabbatar da zaman lafiya da oda a birnin Sokoto da sauran yankunan jihar bayan mutuwar daliba ta aji yu na Kwalejin Shehu Shagari na Ilimi ta Sokoto."

Wani daga cikin tawagar bangaren watsa labarai na gwamnan, wanda ya nemi a sakaya sunansa shima ya tabbatar da saka dokar hana fitar.

Wani sashi cikin sanarwar, ta ambaci Tambuwal na cewa;

"Bayan abin bakin cikin da ya faru a Kwalejin Ilimi ta Shagari a ranar Alhamis da abin da ya biyo baya a birnin Sokoto a safiyar yau zuwa rana, bisa ikon da doka ta bani a sashi na 176(2) na kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya; da sashi na 1 da 4 na Public Order Act; da sashi na 15 na Sokoto State Peace Preservation Law, na ayyana dokar hana fita na awa 24, nan take a birnin Sokoto na tsawon awa 24.

Kara karanta wannan

Sokoto: Mutane sun mamaye tituna da zanga-zanga, sun nemi a saki waɗan da suka kashe ɗalibar da ta zagi Annabi

"Ina kira ga kowa, domin zaman lafiya ya koma gida ya bi wannan doka, da nufin tabbatar da zmaan lafiya, doka da oda a jihar."

Gwamnan ya kara da cewa saba doka ba alheri bane ga kowa.

"Don haka ina kira ga al'umma a kama kai, sannan a girmama doka da oda."

Dalilin saka dokar hana fitar

Wasu mazauna garin Sokoto a safiyar yau, sun fito tituna suna zanga-zanga kama wasu da ake zargin suna da hannu wurin kisar dalibar da yan sanda suka yi.

Yan sandan sun sanar da kama mutum biyu da ake zargi da hannu a kisar yarinyar.

Sarkin Musulmi, Muhammad Sa'ad, shima ya fitar da sanarwa yana alawadai da lamarin kuma ya yi alkawarin gwamnati za ta yi bincike.

'Batanci: Bayan Buhari Ya Yi Allah Wadai Da Kisan Deborah a Sokoto, Osinbajo Ya Yi Magana Da Kakkausar Murya

A wani rahoton, Yemi Osinbajo, Mataimakin Shugaban Kasar Najeriya ya yi alawadai da kisan Deborah Samuel, dalibar aji biyu ta Kwalejin Ilimi ta Shehu Shagari da ke Sokoto bisa zarginta da batanci, rahoton The Guardian.

Kara karanta wannan

'Batanci: Jakadiyar Birtaniya Ta Ce Dole a Hukunta Waɗanda Suka Kashe Ɗalibar Sokoto

Ya nuna alhininsa ne yayin tattaunawa da manema labarai a ranar Juma’a a bangaren jirgin shugaban kasa da ke filin jirgin Nnamdi Azikwe a Abuja, bayan dawowarsa daga Uyo, Jihar Akwa Ibom.

Ya bayyana jin dadinsa akan yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari da Sultan din Sokoto su ka nuna rashin jindadinsu akan lamarin.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel