Ta'addanci: 'Yan ta'adda sun bindige jami'an 'yan sanda har 3 a jihar Neja
- Wani mummunan labari da muke samu ya bayyana yadda wasu 'yan ta'adda suka yiwa jami'an tsaro kwanton bauna
- Sun hallaka jami'an 'yan sanda uku tare da wani dan banga a wani yankin jihar Neja ta Arewa masu Yamma
- Shugaban gundumar Suleja a jihar ya tabbatar da faruwar lamarin, sai dai har yanzu 'yan sanda basu ce komai ba
Jihar Neja - Wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kashe ‘yan sanda uku da wani direban babur a garin Suleja na jihar Neja.
Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 11 na daren ranar Alhamis.
Rahotanni sun ce ‘yan sandan sun amsa kiran gaggawa ne a lokacin da aka yi musu kwanton bauna a kusa da wani wuri da ake kira Old Barracks.
Wata majiya ta ce:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"'Yan bindigar sun yi musu kwanton bauna, wadanda da alama suna tsammanin isowarsu."
Shugaban gundumar Suleja, Abdullahi Shuaibu Maje, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce kimanin mutane uku ne suka tsira daga harin, ciki har da dan banga.
Ya ce yanzu haka suna jinya a wani asibiti da ke yankin.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Wasiu Abiodun, bai amsa kiran waya ba kana bai mayar da sakon tes da aka tura masa ba har zuwa lokacin hada wannan rahoton.
Sojoji 6 sun kwanta dama yayin da yan bindiga suka farmaki wani kauyen a Taraba
Rahotanni sun kawo cewa sojoji shida sun mutu a wani hari da yan bindiga suka kai kauyen Tati da ke karamar hukumar Takum ta jihar Taraba.
An tattaro cewa yan bindigar sun zo ne da yawansu sannan suka farmaki kauyen a ranar Talata da misalin 10 na dare.
Jaridar The Cable ta rahoto cewa maharan sun fafata da dakarun bataliya ta 93 a wani musayar wuta.
Sai dai yan bindigar sun sha karfin yan ta’addan, inda suka kashe sojoji shida da sace wani babban jami’i daya.
Sama da tubabbun 'yan ta'adda 51,000 da iyalansu ke hannunmu, Rundunar sojin Najeriya
A wani labari na daban, mun ji cewa fiye da tubabbun 'yan ta'adda 51,000 da iyalansu ne suka zub da makamansu ga sojojin yankin Arewa maso Gabas kamar yadda sojojin suka bayyana.
Kwamandan rundunar operation Hadin Kai, Manjo Janar Chris Musa, ya bayyana wa Channels TV yayin tattaunawar da suka yi da shi a ranar Litinin.
Ya bayyana yadda mazauna yankin suka dinga taimakon sojoji, musamman yadda suka samu bayanan sirri duk da cewa akwai bangaren da aka sanya wa shamakin sadarwa.
Asali: Legit.ng