Kai tsaye: Shugaba Buhari na zaman bankwana da Ministocinsa da sukayi murabus

Kai tsaye: Shugaba Buhari na zaman bankwana da Ministocinsa da sukayi murabus

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya shiga zaman bankawana da ministocinsa dake son takara kujerun siyasa
  • Shugaban Buhari ya byanna musu cewa nan ba da dadewa ba zai nada sabbin ministocinsu da zasu maye gurabensu
  • Akalla mutum goma ne suka bayyana niyyar takara kujerun siyasa daban-daban

FCT Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari yanzu haka yana ganawa da ministocinsa dake neman takaran siyasa a zaben 2023.

Wannan zama ya biyo bayan umurnin da shugaban kasan ya yiwa dukkan ministoci da masu mukamin siyasa dake da niyyar takara su yi murabus kafin ranar Litinin, 16 ga Mayu, 2022.

Wadanda ke hallare sun hada da Karamin Ministan Ma'adinai da karafuna, Uche Ogar; Karamin Ministan Man fetur, Timipre Sylva; Minister kwadago, Chris Ngige;Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi da Ministar harkokin mata, Pauline Tallen.

Kara karanta wannan

Na rantse babu wanda zai saci ko kwabo idan na zama shugaban kasa, Atiku

Sauran sune Ministan Niger Delta, Godswill Akpabio; Ministan Shari'a, AGF Abubakar Malami da Minister Kimiyya da Fasaha, Ogbonnaya Onu

Jerin Ministocin da sukayi ayyana niyyar takkarar:

Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi (Mai neman kujeran shugaban kasa)

Ministan Niger Delta, Godswill Akpabio; (Mai neman kujeran shugaban kasa)

Minister kwadago, Chris Ngige; (Mai neman kujeran shugaban kasa)

Ministan Kimiyya da Fasaha, Ogbonnaya Onu (Mai neman kujeran shugaban kasa)

Karamin Ministan Ilmi, Emeka Nwajiuba(Mai neman kujeran shugaban kasa)

Karamin Ministan Man fetur, Timipre Sylva(Mai neman kujeran shugaban kasa)

Karamin Ministan Ma'adinai da karafuna, Uche Ogar (Mai neman kujeran gwamnan jihar Abia)

Ministar harkokin mata, Pauline Tallen (Mai neman kujeran Sanata)

Ministan Shari'a, AGF Abubakar Malami (Mai neman kujeran gwamnan jihar Kebbi)

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: Gwamnan El-Rufa'i ya haramta zanga-zanga da sunan addini a jihar Kaduna

Karamin ministan Neja Delta, Tayo Alasoadura (Mai neman kujeran Sanata)

Asali: Legit.ng

Online view pixel