Da Duminsa: Hukumar sojojin Najeriya ta kama wani Soja dake siyarwa yan bindiga makamai a Zamfara

Da Duminsa: Hukumar sojojin Najeriya ta kama wani Soja dake siyarwa yan bindiga makamai a Zamfara

  • Hukumar sojojin Najeriya ta kama wani Soja dake sayarwa yan bindiga makamai da kayan sojoji a jihar Zamfara
  • Rahotanni sun bayyana cewa an kama sojan ne yana shirin sayar da Alburusai 1,000 kan kudi Naira miliyan ɗaya
  • Kakakin rundunar sojin Najeriya, Onyema Nwachukwu, ya ce a halin yanzun ba shi da masaniya kan samun wannan nasarar

Zamfara - Rundunar sojin Najeriya ta yi nasarar kama wani Sojanta da alburusai 1,000 da nufin zai sayarwa yan ta'adda kan kudi Naira miliyan N1m, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Sojan da aka kama da zargin yana aiki ne a barikin sojoji FOB da ke sansani a Galadi, ƙaramar hukumar Shinkafi a jihar Zamfara, kuma ya shiga hannu ne bisa sayar da Alburusai da Kakin sojoji ga yan bindiga.

Kara karanta wannan

Sojan da aka kama yana sayarwa yan bindiga makamai a Zamfara ya fallasa sunayen wasu Sojoji

Sojna Najeriya.
Da Duminsa: Hukumar sojojin Najeriya ta kama wani Soja dake siyarwa yan bindiga makamai a Zamfara Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Wasu bayanai da suka fito daga wata jarida sun nuna cewa Sojan mai suna Bala Nura (19NA/78/3870) ya shiga hannun dakarun tsaro ne ranar Laraba.

Wata majiya ta ƙara da cewa sojan ya amsa laifinsa da cewa yana sayarwa yan ta'addan Alburushi guda 100 mai nauyin 7.62mm a kan kudi Naira N100,000.

Majiyar ta ce ya shiga hannu tare da Alburusai 1,000 waɗan da ya yi alƙawarin cefanar wa yan bindigan kan kudi naira miliyan ɗaya.

Sanarwan kama sojan ta ce:

"An kama wani Soja da ake zargin yana sayarwa yan bindiga Alburusai yayin bincike kan ɓatan wasu Alburusai a sansanin soji FOB da ke Galadi a Shinkafi."
"Sojan mai suna Bala Nura da ke aiki a nan FOB yana da hannu a siyarwa yan bindiga alburusan kuma ya amsa cewa yana sayar da guda 100 kan N100,000. Haka nan ya yi alkawarin sayar da 1,000 kan miliyan ɗaya."

Kara karanta wannan

Jerin sunayen Jaruman Kannywood da suka fito takara da kujerun da suke nema a 2023

Amma yayin da jaridar ta tuntubi mai magana da yawun rundunar sojin Najeriya, Birgediya Janar Onyema Nwachukwu, ya ce ba shi da masaniya kan samun wannan cigaban.

A wani labarin na daban kuma Wani Jirgin sama ɗauke da Fasinjoji 11 ya yi hatsari a cikin Daji

Wani ƙaramin jirgin saman fasinja ya yi hatsari a wani daji da ke kudancin babbar birnin ƙasar Kamaru, Yaounde.

Ma'aikatar kula da sufuri ta ƙasar ta sanar da cewa jirgin mai ɗauke da Fasinja 11 ya yi haɗarin ne ranar Laraba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262