Sunayen Soji 6 da yan bindiga suka kashe a harin kwantan bauna a Taraba

Sunayen Soji 6 da yan bindiga suka kashe a harin kwantan bauna a Taraba

Yan bindiga sun kashe sojoji shida yayin da suke hanyar su ta zuwa wurin da aka kai hari a Tati, wani ƙauye da ke karamar hukumar Takum, a cewar Kakakin Sojin Najeriya cikin wani sakon da ya fitar.

Hakazalika suka sace Kwamandan rundunar, Laftanan Kanal Ememike S. Okore (N/11717).

Kakakin hukumar Sojin Najeriya, Onyema Nwachukwu, a jawabin da ya fitar ranar Laraba ya bayana cewa rundunar 93 Bataliya sun shiga neman Sojan da aka sace don cetosa.

Jaridar Premium Times ta rahoto cewa takardar ta ce lamarin ya faru ne misalin ƙarfe 10 na safiyar ranar 10 ga watan Mayu. Ta ce yan bindigan sun fi sojojin yawa sosai.

Takardar ta kuma ce ba za a iya tabbatar da adadin wadanda suka mutu a bangaren yan bindigan ba.

Kara karanta wannan

Yayin da zaben 2023 ya karaso, EFCC ta shiga binciken kudin PDP da APC a bankuna

Ga jerin sunayen Sojojin da suka rasa rayukansu, kamar yadda Sahara Reporters ta tattaro:

  1. Dauda Tata (7NA/44/4046),
  2. Yusuf Salihu (95NA/40/5031),
  3. Ndubuise Okonkwo (96NA/42/6911),
  4. Abdullahi Ibrahim (13NA/70/7901),
  5. Emmanuel Jerry (14NA/72/14051)
  6. Sani Isa (14NA/72/15462)

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sunayen Soji
Sunayen Soji 6 da yan bindiga suka kashe a harin kwantan bauna a Taraba
Asali: Facebook

Hoton Kwamandan Sojin da yan bindiga suka sace a Taraba ya bayyana

Hoton Kwamandan Sojin Najeriya, Laftanan Kanal Ememike S. Okore (N/11717) da tsagerun yan bindiga masu garkuwa da mutane suka sace a jihar Taraba ya bayyana.

Sahara Reporters a rahoto tace an yi awon gaba da Ememike Okore ne sakamakon harin kwantan baunan.

Kakakin hukumar Sojin Najeriya, Onyema Nwachukwu yace:

"Sojoji yanzu haka na bibiyan yan bindigan kuma ba zasu yi kasa a gwiwa ba wajen ceto jami'in da ya bace"

Asali: Legit.ng

Online view pixel