Yanzu-Yanzu: Buhari Ya Roƙi ASUU Ta Janye Yajin Aiki, Ya Ba Wa Ɗalibai Haƙuri

Yanzu-Yanzu: Buhari Ya Roƙi ASUU Ta Janye Yajin Aiki, Ya Ba Wa Ɗalibai Haƙuri

  • Fadar shugaban kasa ta saka baki kan kai-kawo da ake yi tsakanin gwamnatin tarayya da ASUU wanda ya janyo yajin aiki
  • Shugaba Muhammadu Buhari a rokonsa ya bukaci kungiyar malaman jami'o'in ta dakatar da yajin aikin da ta ke yi
  • Shugaban kasar ya ce janye yajin aikin shine abin da zai fi zama alheri ga daliban jami'o'i, ya kara da cewa gwamnati za ta warware matsalar

Fadar Shugaban Kasa - Domin amfanin dalibai, Shugaba Muhammadu Buhari, a ranar Alhamis, 12 ga watan Mayu, ya bukaci kungiyar malaman jami'o'i, ASUU, ta janye yajin aikin da ta ke yi.

The Nation ta rahoto cewa Shugaba Buhari ya yi wannan rokon ne wurin wani taro na ayyuka da bada lambar yabo a gidan gwamnati, a Abuja.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Shugaban Hadaddiyar Daular Larabawa ya rigamu gidan gaskiya

Yanzu-Yanzu: Buhari Ya Roƙi ASUU Ta Janye Yajin Aiki, Ya Ba Wa Ɗalibai Haƙuri
Buhari Ya Roƙi ASUU Ta Janye Yajin Aiki, Ya Ba Wa Ɗalibai Haƙuri. Hoto: TVC.
Asali: Twitter

A cikin wata sanarwa da Buhari Sallau, hadimin shugaban kasa ya fitar ya ce:

"Ingantaccen ilimi ba wai ga tattalin arziki kawai ya ke da amfani ba, yana da amfani da mutanen kasa.
"Rashin kulawa da ayyuka masu amfani da ilimi ke kawo wa zai cutar da jikokinmu da za su zo a gaba, da kuma wanzuwar talauci da rashin walwala.
"Zai yi wahala mu inganta tattalin arzikinmu da ayyuka masu amfani, ba tare da habbaka bangaren ilimin mu ba."

Buhari ya tuna wa mutane lokacin da bada umurni a ranar 1 ga watan Fabrairu cewa ministan ilimi, Adamu Adamu, da na kwadago, Chris Ngige su zauna da kungiyar don magance matsalar.

Ya kuma yi kira ga kungiyar daliban Najeriya, NANS, ta yi hakuri yayin da gwamnatinsa ke aiki domin warware matsalar.

Kara karanta wannan

Sokoto: Tambuwal ya umarci a yi bincike kan kashe dalibar kwalejin da ta zagi Annabi

Tamkar ASUU, SSANU Da NASU Sun Gabatarwa FG Tsarin Biyan Albashi Da Suke So

A wani labarin, Kwamitin Hadin Gwiwa ta Kungiyar Manyan ma’aikatan jami’o’i (SSANU) da kuma Kungiyar Ma’aikatan Jami’o’i marasa koyarwa (NASU) ta gabatar wa Gwamnatin Tarayya kafar da ta ke so a dinga biyan ma’aikatanta albashi, Leadership ta ruwaito.

A ranar Talata kungiyar ta gabatar wa Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu, kafar University Peculiar Payroll System (U3PS) a Abuja.

Dama tun farko kungiyoyin guda biyu kamar yadda Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU), sun ki amincewa da kafar Integrated Payroll anda Personnel Information System (IPPIS), wacce Gwamnatin Tarayya ta gabatar musu don biyan ma’aikata albashi.

Yayin da ASUU ta zo da kafar University Transparency Accountability System (UTAS), JAC din SSANU da NASU ta kawo U3PS.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164