Da dumi: Kungiyar Malaman COE na Najeriya zasu shiga yajin aiki, sun ba FG makonni 3

Da dumi: Kungiyar Malaman COE na Najeriya zasu shiga yajin aiki, sun ba FG makonni 3

  • Gamayyar Malaman makarantun ilimi COEASU zasu bi sahun takwarorinsu na jami'a da Poly, zasu shiga shiga yajin aiki
  • Shugabannnin kungiyar Malaman kwaljin Ilimi sun baiwa gwamnatin tarayya makonni uku ta cika alkawuransu
  • A cewarsu, gwamnati na musu hanya-hanya bisa yarjejeniyar da suka yi kuma rainin hankalin ya isa

FCT Abuja - Kungiyar Malaman kwalejin ilmin na Najeriya (COEASU) ta baiwa gwamnatin tarayya kwanai 21 ta cika alkawuranta ko su shiga yajin aiki.

Wannan shine shawaran da majalisar zartaswar kungiyar ta yanke a zamanta.

Shugaban kungiyar, Dr Smart Olugbeko da Sakatarenta, Dr Ahmed Bazza,suka fitar da jawabi bayan zaman a birnin tarayya Abuja, rahoton NAN.

A cewar jawabin, muddin gwamnati bata biya musu bukatarsu nan da karshen watan nan ta mayu ba, zasu bi sahun ASUU, NASU, SSANU da ASUP.

Kara karanta wannan

A hukumance: Jita-jita ta kare, Saraki ya bayyana tsayawa takara, ya fadi dalilai

Jawabin yace:

"Majalisar zartaswar kungiyarmu ta zanna a kwalejin ilman tarayya dak Okene, jihar Kogi ranar 6 ga Mayu domin tattauna shawarar da dukkan rassanmu a fadin tarayya suka yanke."
"Mun sake nazari cikin gaskiyar gwamnati wajen sulhu. Mun lura cewa gwamnatin tarayya bata yiwa kungiyarmy adalci ba duk da lokacin da muka bata."
"Gwamnati ta ki cika alkawarin da tayi na gyaran makarantunmu N15bn."

Kungiyar ta kara da cewa gwamnati na mata wasa da hankali kan yarjejniyar da sukayi tun 2010.

Da dumi: Kungiyar Malaman COE
Da dumi: Kungiyar Malaman COE na Najeriya zasu shiga yajin aiki, sun ba FG makonni 3
Asali: UGC

Malaman makarantun Poly sun bi sahu, ASUP ta sanar da shiga yajin aiki

Dazu kun kawo muku cewa kungiyar Malaman makarantun fasaha a Najeriya ASUP ta sanar da cewa ta yanke shawaran shiga yajin aikin gargadi na makonni biyu fari daga ranar 16 ga Mayu, 2022.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa a 2023: Tinubu zai koma gida idan ya fadi zabe - Babachir

Punch ta ruwaito cewa ASUP ta bayyana hakan a jawabin da ta fitar ranar Laraba.

A cewar jawabin, Malaman na Poly sun yanke shawarar shiga yajin ne bayan zaman majalisar zartaswar kungiyar da akayi ranar Laraba

Asali: Legit.ng

Online view pixel