Da Dumi-Dumi: Kotu ta ba da umarnin kama mataimakin Sufetan yan sanda na ƙasa da SP

Da Dumi-Dumi: Kotu ta ba da umarnin kama mataimakin Sufetan yan sanda na ƙasa da SP

  • Wata Kotu a Ogun ta umarci a tsare mataimakin Sufeta Janar (AIG) na shiyya ta 2 da Sufurtandan yan sanda a gidan gyaran Hali
  • Alkalin Kotun, Mai shari'a Ogunfowora, ya ɗauki wannan matakin ne bayan sun yi fatali da umarninsa, ya ce hakan raina sashin shari'a ne
  • Manyan yan sandan biyu sun shiga halin ne bayan ƙin sakin Fasfon wani ɗan China da suka tsare da zargin aikata babban laifi

Ogun - Babbar Kotun jihar Ogun ta ba da umarnin tsare mataimakin Sufeta Janar na yan sanda, hedkwatar shiyya ta 2, Onikan, jihar Legas da kuma Sufurtanda, Tijani Taofiq, bisa raina Kotu.

Manyan jami'an yan sandan sun yi watsi da umarnin Kotu wanda ya bukaci AIG ya biya N500,000 yayin da Sufurtanda Taofiq zai biya N50,000 na diyyar ɓata sunan da suka yi wa wani ɗan China, Chen Zheng.

Kara karanta wannan

Cikakken Labari: Wani Bam Ya Tashi a Masallaci Yayin da Mutane ke tsaka da Sallar Jumu'a

Punch ta rahoto cewa jami'an sun damƙe ɗan China bisa zargin aikata babban laifi kuma daga bisani suka kwace Fasfo ɗinsa.

Babbar Kotu a jihar Ogun.
Da Dumi-Dumi: Kotu ta ba da umarnin kama mataimakin Sufetan yan sanda na ƙasa da SP Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Mai Shari'a Olugboyega Ogunfowora na babbar Kotun Ogun ya umarci a cigaba da tsare jami'an a gidan Yarin Ibara da ke Abeokuta har sai kayyakin ɗan Chana sun dawo.

A hukuncin da ya yanke ranar 9 ga watan Mayu, Alkalin ya umarci a saki Fasfon mutumin mai lamba No.EB4555829.

Ogunfowora ya yi gargaɗin cewa rashin bin umarnin Kotu na sakin Fasfon da kuma biyan tarar da aka wa Jami'an raini ne kuma laifi ne da ke kunshe da hukunci a kundin mulkin ƙasa.

Na tsawon yaushe za'a tsare yan sandan?

A hukuncin da ya yanke ranar Laraba, Ogunfowora, ya umarci a cigaba da tsare manyan yan sandan a gidan Yari har zuwa lokacin da aka sako Fasfon Ƙasa da ƙasa na ɗan China.

Kara karanta wannan

Gara ku biya kuɗin fansar Fasinjojin jirgin kasa da ku sayi Fom ɗin takara a 2023, Sheikh Gumi

Da yake jawabi ga manema labarai jim kaɗan bayan zaman Kotun, Lauyan wanda ya shigar da ƙara, Seun Akinbiyi, SAN, ya yaba da furucin Kotu.

Akinbiyi ya ƙara da cewa irin wannan hukuncin zai sa mutane su amince cewa ɓangaren shari'ar ƙasar nan shi ne gatan mutumin da be da kowa.

Ya ce:

"Da izinin Allah zamu zuba ido mu ga yadda za'a aiwatar da umarnin Kotu, wannan ɗaurin da Kotu ta yi wa AIG da Sufurtanda, zamu ga yadda zai karkare."

A wani labarin kuma Bam ya tashi a kusa da sansanin Sojojin Najeriya a babban birnin jihar Taraba

Wani abu ya sake fashewa karo na uku a baya bayan nan a jihar Taraba da ke arewa ta tsakiya a Najeriya.

Sai dai wannan karon, bayanai sun nuna cewa fashewar ta auku ne a kusa da Hedkwatar sojoji amma babu wanda ya rasa rayuwarsa.

Kara karanta wannan

Wani Bam ya ƙara tashi mutane na tsaka da holewa a jihar Kogi, rayuka sun salwanta

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262