Wata mata ta daɓa wa tsohon saurayinta wuka kan N500 a jihar Ondo
- Wata mata uwan biyu da bata da aure ta daɓa wa tsohon saurayinta wuƙa bayan rikici ya ɓarke tsakanin su a Ondo
- Bayanan matar ya nuna cewa Mutumin ya nemi kwana da ita a gidanta bayan ya ba ƴaƴanta N500 ita kuma ta ƙi yarda, ya kama jibgarta
- Tuni yan sanda suka yi ram da ita kuma suka gurfana a gaban Kotu bisa zargin raunata mutumin
Ondo - Wata mata yar kimanin shekara 39 kuma uwan biyu, Seun Sola, ta daɓa wa tsohon saurayinta, Lomi Alara Akinbinu, wuka a ciki kan N500 a garin Ondo, jihar Ondo.
Matar mai sana'ar siyar da abinci ta shiga hannu kuma an gurafanar da ita gaban Kotu bisa zargin raunata mista Alara ba bisa ƙa'ida ba, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
Wacce ake zargin ta daɓa wa mutumin wuƙa ne lokacin da faɗa ya kaure a tsakanin su a yankin kasuwar Iyalaje da ke garin Ondo.
Bayanan da suka fito daga wurin yan sanda sun nuna cewa matar da ake zargin da kuma mutumin sun ƙaunaci junan su kafin daga bisani su rabu kowa ya kama gabansa.
A cewar wani shaidan gani da ido lamarin ya faru ne lokacin da Mutumin ya ziyarci Seun, ba zato ya haɗu da sabon saurayinta kuma hakan ya tunzura shi.
Nan take ya nemi ta kori sabon saurayinta yayin da yake son su kwana tare amma ta ƙi daga nan faɗa ya kaure a tsakanin su.
Matar da bayyana dalilinta
Punch tace Seun yayin da take faɗin dalilinta na daɓa masa wuka ta ce:
"Tsohon saurayi na ya zo gidana ya ba 'ya'yana N500 su ci abinci, da yamma ya dawo ya faɗa mun zai zo mu kwana tare amma na shaida masa bana sha'awar kasancewa da shi."
"Sai ya nemi na biya shi kudin da ya baiwa ƴaƴana nan take na ba shi. Ba zato ya kama duka na saboda ya zo ya ga sabon saurayina a gidan.
"Hakan ya fusata shi ya hau kaina da duka. Da na fahimci ya fi karfi na sai na yi amfani da wuƙa na caka masa a ciki."
Wane matakin yan sanda suka ɗauka?
Wata majiya ta ce nan da nan a kayi gaggawar kai mutumin Asibiti a Ondo domin kula da lafiyarsa yayin da jami'ai suka kama matar.
A halin yanzun an gurfanar da ita a gaban Kotu bisa zargin raunata tsohon saurayinta da wuƙa. Ta kuma musanta tuhume-tuhumen da ake mata a Kotu.
A wani labarin kuma Jirgin ƙasa ya yi ciki da wata Motar Bas makare da Fasinjoji bayan Direba ya ƙi jin shawara
Jirgin kasa ya kaɗe wata Motar Bas ta haya ɗauke da Fasinjoji yayin da ya zo wucewa a Ilupeju bye-pass jihar Legas.
Rahoto ya nuna cewa Direban Motar ne ya ki bin umarnin jami'an ba da hannu, Fasinjojin Motar sun yi kokarin direwa daga ciki.
Asali: Legit.ng