Billahil lazi la ilaha illahuwa za mu rike maka amanarka – Gawuna ga Ganduje
- Mataimakin gwamnan jihar Kano, Nasiru Yusuf Gawuna, ya yi rantsuwa da Allah cewa zai rikewa Gwamna Abdullahi Ganduje amanarsa
- Gawuna ya dauki alwashin ne a yayin da gwamnan ya gabatar masu da fom din takarar gwamna shi da Murtala Garo
- Ya kuma roki 'ya'yan jam'iyyar APC da kada su kawo masu munafirci da cin amana a harkokinsu
Kano - Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya gabatar da fom din takarar gwamna ga mataimakinsa, Nasiru Yusuf Gawuna da tsohon kwamishinansa, Murtala Sule Garo a matsayin abokin takararsa.
Ya gabatar masu da fom din takarar ne a taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a garin Kano a ranar Talata, 10 ga watan Mayu.
Da yake jawabi jim kadan bayan mika musu fom din takarar, Gawuna ya yi godiya ga Ganduje tare da daukar rantsuwar rike ma ubangidan nasa amana, sashin Hausa na BBC ya ruwaito.
Gawuna ya ce:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Billahil lazi la ilaha illahuwa mai girma gwamna za mu rike maka amanarka, za mu yi tafiya irin wadda kake so.
"Kuma bi izinillahi kai ma Allah zai cika maka bukatarka."
Gawuna ya kuma roki ‘ya’yan jam’iyyarsu ta All Progressives Congress (APC), da kada su yi munafinci ko cin amana a lamuransu.
BBC Hausa ta kuma nakalto yana cewa:
"Ina rokon 'yan jam'iyyarmu da muka hadu a nan, na hada ku da girman Allah yadda mai girma gwamna ya hada ni da dan uwana, shi ya san amanar da ke tsakanina da shi, don Allah don Annabi ka da wanda ya kawo mana annamimanci."
2023: Ganduje ya bayyana ainahin dalilin da yasa ya tsayar da Nasiru Gawuna don ya gaje sa
A baya mun kawo cewa gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa yana so mataimakinsa, Nasiru Yusuf Gawuna, ya gaje sa ne saboda biyayyarsa.
Daily Trust ta rahoto yadda gwamnan da wasu shugabannin jam’iyyar suka tsayar da Gawuna domin ya mallaki tikitin takarar gwamna na jam’iyyar APC sannan suka lallashi kwamishinan karamar hukuma, Murtala Sule-Garo ya hakura ya zama abokin takararsa.
An gabatar da hukuncin a taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a ranar Talata sannan aka amince da shi gaba daya.
Asali: Legit.ng